'Ka Ƙaƙaba Mana Dokar Ta Ɓaci Kawai': Dattawan Arewa Sun Roƙi Tinubu Alfarma

'Ka Ƙaƙaba Mana Dokar Ta Ɓaci Kawai': Dattawan Arewa Sun Roƙi Tinubu Alfarma

  • Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta bukaci Bola Tinubu ya dauki mataki mai tsauri kan rashin tsaro da ya addabi al'umma
  • Dattawan sun roke shi da ya ayyana dokar ta baci kan matsalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin
  • NEF ta ce kashe sojoji da fararen hula a jihohi kamar Benue, Niger, Zamfara da Sokoto na nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo karshen rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

Kungiyar ta bukaci ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaro a yankin da ke fama da matsalolin tsaro.

An roki Tinubu ya kakaba dokar ta-ɓaci a Arewa
Dattawan Arewa sun bukaci Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a Arewacin Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yan bindiga sun hallaka sojoji a Arewa

A cikin wata sanarwa da Abubakar Jiddere, mai magana da yawun NEF, ya fitar, ya ce Arewa na fama da kashe-kashe, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Wike da Fubara sun sasanta watanni da dakatar da zababbun shugabannin Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yankin na fama da sabon tashe-tashen hankula daga 'yan bindiga a Arewa ta tsakiya da arewa maso yamma, yayin da arewa maso gabas ke fama da 'yan ta'adda.

Sanarwar ta ce ana yawan kisan jami'an tsaro ba kakkautawa a yankin wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

“Fiye da jami'an tsaro 20, masu kare kasa, an yanka su kamar dabbobi daga gungun 'yan ta’adda da suka kai hari mai karfi.
“Wannan hari mai ban tsoro wani sabon shafi ne cikin jerin kisan gillar da ya maida Arewacin Najeriya wurin yaki tun watan Yuni 2025.
“Daga Benue zuwa Filato, daga Kwara zuwa Kaduna, daga Zamfara zuwa Sokoto da Borno, yanzu kuma Neja ba matsalar tsaro ba ce kawai.
Rashin tsaro ya jawo rokon Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a Arewa
Dattawan Arewa sun taso Tinubu a gaba ta sanya dokar ta-ɓaci. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Dattawan Arewa sun caccaki gwamnatin Tinubu

Jiddere ya ce gwamnatin tarayya ta “gaza matuka kuma akai-akai” wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a wannan yanki, cewar Vanguard.

Ya ce arewa “na nutsewa cikin jini, jama’arta sun zama tamkar an yar da su,” sannan ya ce jami’an tsaro ba su dauki isassun matakai ba.

Kara karanta wannan

NLC ta fusata, ta shirya yamutsa gwamnati a 'yan kwanaki masu zuwa

Ya ce:

“Kungiyar Dattawan Arewa ba za ta sake amincewa da ta’aziyya marar amfani, jawaban da suka ci karo da gaskiya ko sanarwa mara amfani ba.
“In dai gwamnatin tarayya ta ci gaba da jan kafa ko kaucewa matsalar, mutane za su dauka cewa wannan shiru na gwamnati da gangan ne.
“Kungiyar na bukatar a gaggauta ayyana dokar ta baci kan tsaro a duk fadin Arewacin Najeriya ba tare da jinkiri ba.

NEF ta ce a fili take gargadin gwamnati cewa ci gaba da nuna halin ko-in-kula zai iya janyo martani daga jama’a.

Dattawan Arewa sun soki sanya dokar ta-ɓaci

A baya, kun ji cewa Dattawan Arewa sun buƙaci Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta maida Gwamna Simi Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisa kan kujerunsu.

Mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa (NEF), Abubakar Jika Jiddere ya ce babu dalilin ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

NEF ta kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hana rikicin siyasa yaɗuwa zuwa wasu jihohi kamar Kano a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.