'Dalilin da Ya Sa Abacha Ya Gagara Hallaka Mahaifiyar Bola Tinubu a Rigimar 1993'
- Dan marigayi MKO Abiola ya yi magana kan mulkin marigayi Janar Sani Abacha da rigimar zaben 12 ga watan Yunin 1993
- Jamiu Abiola ya ce Abacha ya gagara kashe mahaifiyar Bola Tinubu, Alhaja Abibatu Mogaji, saboda girmamawa da karbuwarta a idon jama'a
- Ya ce Alhaja Mogaji ta yi adawa da soke zaben 1993, har ta cire mayafinta tana rokon Ibrahim Babangida ya soke matakin da ya dauka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ɗan marigayi MKO Abiola ya soki mulkin Janar Sani Abacha musamman game da zaben 12 ga watan Yuni
Jamiu Abiola ya fadi babban dalilin da ya sa Janar Sani Abacha ya gagara hallaka mahaifiyar Bola Tinubu.

Source: UGC
Dan Abiola ya yabawa gwagwarmayar mahaifiyar Tinubu
Dan marigayin ya bayyana haka ne yayin hira ta musamman da jaridar Punch a yau Asabar 28 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan
Bayan hasashe da dama, an gano 'dalilin' murabus din Ganduje daga shugabancin APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'u Abiola ya ce Abacha ya gagara kashe Alhaja Abibatu Mogaji ne saboda girman tasirinta da yadda jama’a ke girmamata.
Jami'u wanda mahaifinsa ne wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 1993 da aka soke ya nuna damuwa kan abubuwan da suka faru.
A yayin hirar, Jamiu ya ce Abacha yana kai hari ne ga mutane da ba su da kariya ko goyon bayan jama’a.
Ya ce marigayin ya gagara kashe ta ne saboda mahaifiyar Tinubu ta shahara a matsayin shugabar ‘yan kasuwa.
Jamiu ya ƙaryata ikirarin tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, da ke cewa Tinubu da mahaifiyarsa sun goyi bayan soke zaben 1993.
Ya ce:
“Wannan zargi ba wai kawai ƙarya ba ne, amma abin takaici ne ga Alhaja Abibatu Mogaji, da ta goyi bayan soke zaben, da ta rasa goyon bayan ‘yan kasuwa."

Source: Getty Images
Jami'u ya kare Tinubu a rikicin zaben 1993
Jami'u ya bayyana cewa Mogaji ta dauki matakin nuna adawa da soke zaben, ciki har da cire mayafinta a bainar jama’a tana roƙon Babangida da ya janye hukuncinsa.

Kara karanta wannan
'An yi ƙulle ƙulle': Jonathan ya faɗi abin da hadimin Yar'Adua ya yi masa da ba zai manta ba
Hadimin shugaban ƙasa ya kuma kare Tinubu kan rawar da ya taka a rikicin 12 ga Yuni, yana mai cewa ya nuna jarumta a lokacin.
“A matsayin Sanata, ya tsaya a zauren majalisa a ranar 19 ga Agusta, 1993, ya kira soke zaben ‘juyin mulki, Wannan jarumta ce ta musamman."
- Cewar Jamiu Abiola
Yayin da ya tuna da irin rayukan da suka salwanta a danginsu, Jamiu ya ce Abacha yana kai hari ne ga waɗanda ba su da kariya da tasiri.
A karshe, Jamiu Abiola ya ce dimokuradiyyar Najeriya ta samu ci gaba ne saboda jarumtaka irin ta Tinubu da mahaifiyarsa a lokacin tarihi.
Matar Abacha ta ƙaryata zargin da ake masa
Kun ji cewa matar marigayi Sani Abacha ta fito ta yi magana kan zargin da ake yi wa mijinta na sace dukiyar Najeriya a lokacin da yake karagar mulki.
Maryam Abacha ta bayyana cewa da gangan aka riƙa yin mummunar fahimta kan yadda tsohon shugaban ƙasan ya gudanar da harkokin kuɗi.
Maryam Abacha ta bayyana cewa ƴan Najeriya suna da matsala domin su kan yarda da dukkanin abin da aka gaya musu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng