Ba Daraja: Sarki Ya Zargi Tsohon Gwamna da Wawure Kason Masarauta kafin Barin Mulki

Ba Daraja: Sarki Ya Zargi Tsohon Gwamna da Wawure Kason Masarauta kafin Barin Mulki

  • Oba na Benin, Mai Martaba, Ewuare II, ya bayyana yadda tsohon Gwamna Godwin Obaseki ya hana fadar masarautar kudin da ake ware mata
  • Sarkin ya ce an fara rage kudin kafin daga baya a dakatar da su gaba daya, yana mai cewa hakan ya zama yunkurin kaskantar da masarauta
  • Oba Ewuare II ya sha alwashin dawo da filayen da aka mamaye tare da kiran a duba kundin tsarin mulki don tabbatar da matsayin sarauta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-City, Edo - Oba na Benin, Mai Martaba, Ewuare II, ya yi zargi tsohon gwamnan Edo, Godwin Obaseki da almundahana.

Sarkin ya bayyana yadda Godwin Obaseki, ya hana fadar masarautar kudin da ake ware mata na tsawon wata bakwai.

Ana zargin Obaseki da wawure kudin masarauta
Sarkin Benin ya zargi Obaseki da almundahana da kudin masarauta. Hoto: Gov. Godwin Obaseki.
Source: Facebook

An zargi gwamna Obaseki da kwashe kuɗin masarauta

Kara karanta wannan

Wike da Fubara sun sasanta watanni da dakatar da zababbun shugabannin Ribas

Sarkin ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a jihar, kamar yadda The Nation ta ruwaito a jiya Juma'a 28 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken ya ce an fara da rage adadin kudin kafin daga baya a daina tura su gaba daya.

Oba Ewuare II ya ce wannan mataki na gwamnatin da ta shige ya kasance yunkuri na kaskantar da fadar masarauta da kuma rage darajarta a gaban jama’a.

Sarki ya koka da rashin tallafawa masarauta

Sarkin ya ce fadar masarautar ita ce ke biyan ma’aikatan fadarsa da kuma kula da tsaftar muhalli a kusa da fada duk da rashin samun kudin gwamnati.

Oba Ewuare II ya jaddada cewa hana kudin da kuma rage su ba tare da wani bayani ba ya kasance yunkuri na nuna halin ko-in-kula ga masarautar.

Ya kara da cewa Allah da kakanninsa ba su bar irin wannan shiri na keta masarauta ya yi nasara ba, duk da yunkurin wasu.

Sarki ya taso Obaseki a gaba kan almundahana
Sarki na zargin Obaseki da kwashe masa kudin masarauta. Hoto: Edo State Government.
Source: Getty Images

Sarki ya bukaci mutunta masarauta saboda darajarta

Sarkin ya kuma tuna yadda wani tsohon Gwamnan soja da masarautar ta taimaka masa da baya ya juya mata baya ta hanyar gini a fili mai tsarki kusa da fada.

Kara karanta wannan

NLC ta fusata, ta shirya yamutsa gwamnati a 'yan kwanaki masu zuwa

Ya rantse da cewa zai dawo da dukkan filayen da aka karbe su da karfi, musamman wadanda suke da alaka da addini ko al’ada.

Yayin da yake magana kan bukatar sauya kundin tsarin mulki, ya ce lokaci ya yi da za a fayyace matsayin sarakunan gargajiya a doka, cewar The Guardian.

Sarkin ya ce sanin matsayin Sarki a tsarin mulki zai taimaka wajen dakile cin zarafi da kuma tabbatar da daidaito wajen tafiyar da masarautu.

Obaseki ya bugi kirji kan ayyukan alheri

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya kaddamar da ayukka da dama da ya yi lokacin da yake mulki.

Obaseki ya bayyana cewa ya gamsu da ayyukan da ya yi wa al'umma a mulkinsa, inda ya ce ya cika alƙawurran da ya ɗauka a lokacin da ya ke mulki.

Tsohon gwamnan ya fadi haka ne ana sauran wasu ƴan kwanaki ya sauka daga kan madafun iko da miƙa mulki ga zababben gwamnan Edo, Monday Okpebholo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.