Zargin Badakalar N80.2bn: EFCC Ta Zargi Yahaya Bello da Barazana ga Shaidanta
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta yi zargin cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello na son kawo cikas a shari'arsa
- EFCC na zargin tsohon gwamnan da karkatar da kudi har Naira biliyan 80.2 daga baitul malin jihar Kogi domin biyan bukatunsa da na iyalansa
- A zaman kotun da ke gudana, EFCC ta ce jami'an tsaron Yahaya Bello sun yi barazana ga daya daga cikin shaidunsu da ke aiki a wani bankin kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta ci gaba da sauraron shari’ar tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC.
Hukumar EFCC ta zargi Yahaya Bello da wawure Naira biliyan 80.2 daga baitul malin Jihar Kogi, sannan ya yi amfani da kudin wajen biyan bukatunsa na kai da iyalansa.

Source: Twitter
A wata sanarwa da hukumar EFCC ta fitar a shafinta na X, ta bayyana cewa tsohon gwamnan na kokarin kawo cikas ga shari’ar da ake yi a halin yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta zargi Yahaya Bello da yin barazana
PM News ta wallafa cewa lauyan masu kara, Kemi Pinheiro (SAN), ya bayyana wa kotu cewa wata daga cikin shaidu na EFCC, Mashelia Aryan Mashelia Bata, ta shiga damuwa.
Ya ce Mashelia na aiki a matsayin jami’i a bankin Zenith, kuma ta fuskanci barazana daga wasu jami’an tsaro da ke aiki tare da wanda ake tuhuma.
Pinheiro ya ce barazanar da aka yi wa shaidar, wacce ke matsayin shaida ta hudu, babbar illa ce ga tsarin shari’ar da ake gudanarwa, yana mai kira da a dauki mataki.
Yahaya Bello ya mayar da martani ga EFCC
A martaninsa, Lauyan Yahaya Bello, J.B. Daudu (SAN), ya bayyana shakku kan zargin, inda ya ce bai tabbatar cewa jami’an tsaron da ake magana a kansu na daga cikin na wanda ake tuhuma ba.
Sai dai babban lauyan ya ce ba zai yi watsi da zargin ba, kuma zai gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Source: UGC
Daudu SAN ya ce:
“Wannan ba shi ne shaidar farko da ke ba da bayani a kotu ba, kuma babu wanda aka taba zargin da cin zarafi. Duk da haka, zan bincika lamarin kuma in dawo da amsa ga kotu a rana mai zuwa. Zan kuma gana da shaidar domin ya bayyana wanda ya ci zarafinsa.”
Hukumar EFCC na ci gaba da tuhumar tsohon gwamnan da laifin karkatar da dukiyar gwamnati da kuma amfani da ita, lamarin da ta ce ya saba doka.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ke jagorantar zaman sauraron karar a kotun.
Kogi: An wawure N1.09bn a cikin kwanaki
A wani labarin, mun wallafa cewa shaidan hukumar EFCC, Mashelia Arhyel Dada, ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya da ke Maitama, Abuja, yadda aka cire N1,096,830,000 daga asusun gwamnatin Kogi.
Shaidan da ke aiki a bankin Zenith, wanda shi ne hudu da EFCC ta gabatar, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 26 ga Yuni, 2025, a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite yayin ci gaba da shari'ar.
Masheliaya fayyace yadda aka rika zare makudan kudade daga asusun gudanarwar gidan gwamnati tsakanin shekarun 2016 zuwa 2023, ta amfani da hanyoyin banki daban-daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

