Shekarar Hijira: Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Rashin Tsaro, Yakin Iran da Isra'ila

Shekarar Hijira: Sarkin Musulmi Ya Yi Magana kan Rashin Tsaro, Yakin Iran da Isra'ila

  • Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya ce sabon yanayin rashin tsaro a Najeriya na kokarin kauce wa duk wata dabara da ake amfani da ita
  • Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bukaci a rungumi addu’a da komawa ga Allah tare da sabunta niyya a Sabuwar Shekarar Hijira
  • Ya kuma yi kira ga shugabannin duniya su dakatar da tashin-tashinar Iran da Isra’ila gaba daya domin zaman lafiya da kwanciyar hankali

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar JNI ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta NSCIA, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yi magana yayin shiga sabuwar shekarar Hijira.

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana damuwa kan yadda hare-hare da rashin tsaro ke bijire wa duk wata dabara ta kawo karshensu.

Kara karanta wannan

Ajiye Shettima a 2027: Kungiyar Sanata Barau ta rikida zuwa 'Tinubu Barau'

Sarkin Musulmi ya bukaci a yi addu'a a sabuwar shekarar hijira
Sarkin Musulmi ya bukaci a yi addu'a a sabuwar shekarar hijira. Hoto: National Moon Sighting Comittee
Source: Facebook

Leadership ta wallafa cewa sakataren JNI na ƙasa, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ya fitar da sanarwar bayan shiga Sabuwar Shekarar Hijira ta 1447AH.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sultan ya yi kira da a tashi tsaye wajen addu’o’i da ibada domin zaman lafiya da tsaron Najeriya da duniya gaba ɗaya.

A dage da ibada a sabuwar shekarar Hijira

Yayin shiga watan Muharram na 1447AH a Najeriya, Sultan ya mika gaisuwa ga dukkan Musulmin ƙasar da na duniya baki ɗaya dangane da Sabuwar Shekarar.

Ya kuma bukaci Musulmi da su kasance masu tsoron Allah, masu tsayawa ga ibada, da bin doka da oda a kowane lokaci.

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira a nisanci shagulgulan da ba su da tushe a cikin addinin Musulunci da kuma yin abubuwan da suka halasta kawai.

Addu’a domin kwanciyar hankali a Najeriya

Sarkin Musulmi ya bukaci da a dage da addu’o’i domin samun saukin halin da ƙasa ke ciki, musamman ma game da matsalar tsaro da ke neman hana ci gaba.

Kara karanta wannan

Rikici ya kare: Tinubu ya gana da Fubara, Wike da 'yan majalisar Rivers a Aso Villa

Ya ce yanayin matsalar tsaro yana nunawa duniya cewa akwai buƙatar ɗaukacin 'yan Najeriya su koma ga Allah tare da neman shiriya da kariya daga gare shi.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Muna roƙon Allah Mai gafara, Mai rahama, ya taimaka wa 'yan gudun hijira Musulmi da waɗanda ke cikin matsanancin hali a duniya,
"Ya dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga duniya baki ɗaya, musamman Najeriya, ya kuma sauƙaƙa wa talakawan Najeriya a fannonin tattalin arziki, zamantakewa da siyasa.”

Kiran Sarkin Musulmi ga shugabannin duniya

Sultan ya kuma yi kira ga shugabannin duniya da su dakatar da rikicin Iran da Isra’ila da sauran tashin-tashinar da ke barazana ga zaman lafiyar duniya.

Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce ci gaba da irin wannan tashin hankali na iya lalata tsarin rayuwa da tattalin arziki.

Sarkin Musulmi ya yi magana kan yakin Iran da Isra'ila
Sarkin Musulmi ya yi magana kan yakin Iran da Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Saudiyya ta sanar da shiga shekarar 1447

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa ranar Alhamis, 26 ga Yuni aka shiga sabuwar shekarar Musulunci.

Hakan na zuwa ne bayan ganin watan Muharram da aka yi a yammacin ranar Larana bayan watan Zul Hijja ya cika kwana 29.

An bukaci mutane su dage da ibada a sabuwar shekarar Musulunci musamman azumin Ashura da ake a watan Muharram.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng