'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Fulani, Sun Harbi Iyalan Shi da AK47
- 'Yan bindiga sun kai hari cikin dare a wani sansanin Fulani da ke Kogi, inda suka sace wani shugabansu mai suna Malam Iliyasu
- Rahotanni da suka fito sun tabbatar da cewa an jikkata matarsa da ɗansa Abdulsalam a yayin da suke ƙoƙarin hana sace shi
- Biyo bayan harin da aka kai, an kwashe iyalan shugaban zuwa asibiti yayin da hukumomi suka gano harsasai 17 na AK-47 a wajen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari cikin dare a wani sansanin Fulani da ke kauyen Shagari, a karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindigar sun sace wani shugaban Fulani mai suna Malam Iliyasu.

Source: Original
Legit ta tattaro bayanai kan harin da aka kai ne a cikin wan sako da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 12:20 na dare a ranar Alhamis, yayin da masu harin suka farmaki gidan Malam Iliyasu.
A yayin harin, 'yan bindigar sun harbi matarsa da ɗansa Abdulsalam a hannu da ƙafa, inda su biyun ke ci gaba da karɓar kulawar likita a asibitin Ashafa da ke kusa.
Yadda aka sace shugaban Fulani a Kogi
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun zo ne da bindigogi kuma suka fara harbe-harbe a sama domin razana mazauna yankin kafin su kutsa cikin gidan Malam Iliyasu.
An ce sun yi masa dirar mikiya ne tare da jikkata matarsa da ɗansa a lokacin da suka yin ƙoƙarin hana su tafiya da Malam Iliyasu, bayan haka, suka fice da shi zuwa inda ba a sani ba.
Wani ɗan uwan wanda aka sace, Alhaji Ahmadu Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai roƙon hukumomi su gaggauta ɗaukar mataki don kubutar da Mallam Iliyasu.
An gano harsasai a gidan shugaban Fulanin
Rundunar tsaro da ta kai samame bayan harin ta gano harsasai 17 da aka harba daga bindigar AK-47 a wajen da lamarin ya faru, lamarin da ke nuna irin yadda harin ya yi muni.
Hukumomin tsaro sun fara gudanar da bincike don gano inda masu garkuwar suka nufa da kuma yadda za a kubutar da wanda aka sace cikin koshin lafiya.

Source: Facebook
Yanzu haka, al’umma da dangin wanda aka sace suna cikin fargaba, inda suka bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara tsaurara matakai don kawo ƙarshen ire-iren waɗannan hare-hare.
Ana fatan jami'an tsaro za su yi aiki domin ceto Malam Iliyasu tare da sauran mutanen da aka sace a jihar.
Za a kashe masu taimakon 'yan bindiga a Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta fara daukar mataki mai tsauri kan 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Gwamnan jihar Kebbi ya bayyana cewa suna shirin kawo dokoki masu tsauri da suka shafi hukuncin kisa ga masu taimakon 'yan bindiga.
Legit ta rahoto cewa gwamnan Kebbi ya yi magana ne yayin da ya kai ziyarar jaje a masarautar Zuru bayan wani harin 'yan bindiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

