'Yan Bindiga Sun Kwace Ikon Karamar Hukuma a Katsina? 'Yan Sanda Sun Yi Bayani
- Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta fito ta yi magana kan rahotannin da ke cewa ƴan bindiga sun ƙwace iko a ƙaramar hukumar Kankara
- A cikin wata sanarwa, ta bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin rahotannin waɗanda aka yaɗa
- Hakazalika ta bayyana cewa za ta ɗauki mataki domin zaƙulo waɗanda ke da hannu a yaɗa labaran
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta yi magana kan rahotannin da ke yawo cewa ƴan bindiga sun ƙwace iko a ƙaramar hukumar Kankara.
Rundunar ƴan sandan ta bayyana rahotannin a matsayin ƙarya, marasa tushe kuma babu gaskiya a cikinsu.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Alhamis a garin Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun ce komai ya lafa a Kankara
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa rundunar ta samu labarin jita-jitar da ke yawo musamman a shafin sada zumunta na X da ke cewa ƴan bindiga sun ƙwace iko a ƙaramar hukumar Kankara.
Ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin rahotannin da aka yaɗa.
"Rundunar ƴan sandan jihar Katsina na so ta jaddada cewa wannan iƙirari ƙarya ce tsagwaronta, babu wani tushe ko makama a cikinsa."
"Wannan jita-jita na da nufin tayar da hankalin jama’a da haifar da ruɗani a cikin al’ummar Kankara da jihar baki ɗaya."
"Muna tabbatar wa da jama’a cewa akwai kwanciyar hankali a ƙaramar hukumar Kankara kuma komai yana ƙarƙashin kulawa."
"Mutane na ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda aka saba ba tare da wata matsala ba. Rundunar ƴan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro suna ci gaba da aiki tuƙuru don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a musamman a Kankara."
"Tun da daɗewa rundunar ta ɗauki matakan rigakafi da suka haɗa da yaƙi da garkuwa da mutane, fashi da makami, da kuma satar shanu, waɗanda ke nuna sakamako mai kyau a fannin tsaro.”
"Don haka muna roƙon jama’a da su yi watsi da wannan ƙarya gaba ɗaya, kuma su nemi sahihan bayanai daga majiyoyin da za a iya dogara da su."
"Haka kuma, muna kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta da su dinga taka tsantsan da bin ƙa’ida wajen yaɗa bayanai."
“Rundunar ƴan sanda na da cikakken ƙuduri na ci gaba da samar da yanayi mai aminci ga kowa da kowa a jihar, kuma za ta ɗauki duk matakan da suka dace domin tunkarar kowanne irin ƙalubale na tsaro.”
"A ƙarshe, rundunar ta fara bincike don gano tushen waɗannan bayanai na ƙarya, kuma za ta ɗauki matakai na doka kan duk wanda aka samu da hannu a yaɗuwar su."
- DSP Abubakar Sadiq

Source: Original
Ƴan bindiga sun sace basarake
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun sace basarake a yayin wani hari da suka kai a jihar Katsina.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya yi magana kai tsaye kan Atiku da El Rufai masu shirin kifar da shi a 2027
Ƴan bindigan sun sace basaraken ne a ƙauyen Kanaka da ke ƙaramar hukumar Ganjuwa ta jihar.
Jami'an tsaro sun fara ƙoƙarin ceto basaraken daga hannun da suka yi awon gaba da shi zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng

