Bayan Kashe Dalibi, an Rufe Jami'ar IBB saboda Matsalolin Tsaro a Neja
- Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya bayar da umarnin rufe Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) da ke Lapai saboda rikicin tsaro
- Rahotanni sun nuna cewa umarnin ya biyo bayan kashe wani ɗalibi a cikin harabar jami’ar a ranar Litinin, 23 ga Yuni, 2025
- Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ana daukar matakan gaggawa don dawo da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'umma
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Gwamnatin jihar Neja ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago ta sanar da rufe Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) da ke Lapai.
Rahotanni sun nuna cewa an rufe jami'ar ne saboda rikicin tsaro da ya janyo asarar rai a cikin harabar makarantar.

Source: UGC
Sanarwar hakan na ƙunshe ne a wani sako da aka wallafa a shafin gwamna Umaru Bago na Facebook a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin ta ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da tsaron ɗalibai da ma’aikata, da kuma ba da damar gudanar da cikakken bincike a kan abubuwan da suka faru.
Dalilin rufe jami’ar IBB a jihar Neja
Sanarwar gwamnatin Neja ta bayyana cewa harin da aka kai a cikin harabar jami’ar da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗalibi a ranar 23 ga Yuni, ya sanya gwamnati cikin matuƙar damuwa.
Punch ta wallafa cewa sakataren gwamnatin jihar ya ce:
“Ana matuƙar bakin ciki da faruwar lamarin, kuma gwamnatin jihar na daukar matakan gaggawa domin dakile rikicin da kuma tabbatar da cewa irin haka ba zai sake faruwa ba,”
Ya kuma buƙaci ɗalibai da ma’aikatan jami’ar da su kwantar da hankali tare da bin dukkan umarnin da hukumomin tsaro za su bayar, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Ana bincike kan kashe dalibin jami'ar IBB
A cewar sakataren, gwamnati ta dukufa wajen gano waɗanda ke da hannu a cikin wannan danyen aiki, tare da tabbatar da cewa doka ta yi aikinta.
Ya kara da cewa:
“Gwamnati ba za ta lamunci duk wani nau’in barna ko tashin hankali da zai jefa rayuwar jama’a cikin hadari ba. Za mu ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da fitar bayani kan halin da ake ciki daga lokaci zuwa lokaci, yana mai roƙon jama’a da su kasance masu haƙuri da jajircewa

Source: Facebook
Rahotanni daga jami’ar sun nuna cewa lamarin ya tayar da hankali tsakanin ɗalibai da ma’aikata, inda da dama daga cikinsu suka fara barin harabar makarantar kafin matakin gwamnatin.
Wani ɗalibi da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa:
“Mun tsorata matuƙa da kashe ɗalibin, kuma muna fatan gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace domin kare sauran rayuka.”
Jami'o'in 3 a Najeriya sun yi fice a duniya
A wani rahoton, kun ji cewa an fitar da wani rahoto da ya nuna makarantun da suka fi nagarta a fadin duniya.
A Najeriya, jami'o'i uku ne suka samu shiga jerin makarantun ciki har da jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Rahoton ya nuna cewa Najeriya bata taka rawar gani sosai ba idan aka kwatanata da rawar da wasu kasashen Afrika suka taka a bana.
Asali: Legit.ng


