Sokoto: Gwamna Ya Ƙaddamar da Kasuwar Sauƙi saboda Al'umma, Za a Yi Gwanjon Abinci

Sokoto: Gwamna Ya Ƙaddamar da Kasuwar Sauƙi saboda Al'umma, Za a Yi Gwanjon Abinci

  • Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto ya ƙaddamar da “Shagon Sauki Na Amadun Alu” domin ma’aikata da 'yan fansho
  • Ahmad Aliyu ya ce gwamnati za ta rage farashin kayan abinci da kashi 20 cikin ɗari, don rage raɗaɗin cire tallafin mai
  • Ya jaddada cewa wannan ba gasa da 'yan kasuwa ba ne, illa dai tallafa wa marasa galihu da karancin samun abinci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya kawo sauki ga al'ummar jiharsa duba da halin da ake ciki.

Gwamna Aliyu ya ƙaddamar da wani shiri na musamman na tallafin abinci da aka kira “Shagon Sauki Na Amadun Alu,”.

Gwamna ya kaddamar da kasuwar sauki
Gwamna ya bude kasuwar sauki ga ma'aikata. Hoto: Sokoto Government House.
Source: Facebook

Gwamna ya duba halin da ma'aikata ke ciki

Hadimin gwamnan, Hon. Nasser Bazzar shi ya wallafa hakan a Facebook inda aka ce an tanadi shirin ne ga ma’aikata da ma’aikatan ƙananan hukumomi da 'yan fansho.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue ya fusata da kisan matafiya 'yan Kano, ya sha alwashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin gwamnatin jihar wanda ke nufin “Shagon Rangwamen Mulkin Aliyu,” an ƙirƙire shi don saukaka samun kayan abinci masu muhimmanci da rangwamen farashi.

A wajen ƙaddamar da shirin a Sokoto ranar Laraba, Aliyu ya ce wannan mataki yana nuna cikakken jajircewarsa ga jin daɗin ma’aikata da masu karamin karfi.

A karkashin wannan tsari, gwamnati za ta bayar da rangwamen kashi 20 cikin ɗari ga farashin kayan abinci.

Ya ce:

“Wannan shiri na da nufin rage nauyin da jama’a ke fuskanta ta hanyar ba da kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, mai da makaroni.
“Misali, buhun shinkafar Dangote mai nauyin 50kg da ake sayarwa ₦75,000 a kasuwa, yanzu za a sayar da shi ₦60,000, yayin da shinkafa ta gida za ta kasance ₦50,400 maimakon ₦63,000.
"Gero (100kg) zai koma ₦52,000 maimakon ₦65,000, sannan jarkar man girki za ta koma ₦13,240 daga ₦16,550."
Gwamna ya tausayawa al'ummarsa saboda halin kunci
Gwamna Ahmad Aliyu ya kaddamar da kasuwar sauki a Sokoto. Hoto: Office of the Press Secretary, Government House, Sokoto.
Source: Twitter

Yankunan da za a fara shirin gwanjon abinci

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Shugaba Tinubu ya gabatar da abokin karatunsa a Amurka ya ƙayatar da jama'a

Farkon aiwatar da shirin zai fara a ƙananan hukumomi shida: Sokoto ta Arewa, Sokoto ta Kudu, Wamakko, Bodinga, Dange Shuni da Kware, sauran za su biyo baya.

Aliyu ya bayyana cewa shirin ba gasa ba ne da ‘yan kasuwa, illa kawai taimako ne na wucin gadi ga marasa galihu.

Ya yaba wa ‘yan kasuwar jihar Sokoto bisa goyon bayan da suke bayarwa tare da roƙon al’umma su rungumi shirin da hannu bibiyu.

Ya kuma ambaci Gwamna Umar Namadi na Jigawa a matsayin wanda ya ba da kwarin gwiwa wajen ƙirƙirar shirin.

“Ina godiya da wannan tunani da Malam Namadi ya bayar, kuma ya karfafa mini guiwa wajen kafa wannan domin amfanar al’umma."

- Cewar Gwamna Ahmad Aliyu

Gwamna ya magantu kan sulhu da yan bindiga

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin Sokoto ta bayyana sulhu da ƴan bindiga da suka miƙa wuya a matsayin dabarar magance ta'addanci.

Hadimin Gwamna Ahmed Aliyu kan tsaro, Kanar Ahmed Usman (rtd), ya ce dabara ce ta tsaro ta sa suka nemi sulhu ba tsoro ba.

Gwamnati ta ce za ta ci gaba da amfani da ƙarfin bindiga ga 'yan ta'adda a inda ya kamata, amma ta buɗe ƙofar sulhu ga masu mika wuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.