Sabuwar Shekarar Musulunci: Gwamnatin Jihar Kwara Ta Ayyana Ranar Hutu

Sabuwar Shekarar Musulunci: Gwamnatin Jihar Kwara Ta Ayyana Ranar Hutu

  • Gwamnatin jihar Kwara ta ba da hutu domin shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1447 bayan Hijira daga Makka zuwa Madina
  • A cikin sanarwar da aka fitar, gwamnatin ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar hutu a faɗin jihar saboda muhimmancin ranar
  • Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya buƙaci al'ummar jihar da su yi koyi da darussan da ke cikin Hijirar Annabi Muhammad SAW

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta ayyana ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1447 bayan Hijira.

Gwamnatin ta ayyana ranar Alhamis, 26 ga Yuni, 2025 a matsayin rana mai hutu ga ma’aikata a fadin jihar, domin shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 bayan Hijira.

Gwamnatin Kwara ta ba da hutun shigowar sabuwar shekarar musulunci
Gwamnatin Kwara ta ayyana ranar hutu saboda shigowar shekarar musulunci Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Rafiu Ajakaye, ya fitar a madadin gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

Kara karanta wannan

1447 AH: Gwamna Kirista ya ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci a jiharsa

Gwamnatin Kwara ta ba da hutun sabuwar shekara

A cewar sanarwar, gwamnan ya amince da ayyana ranar Alhamis, wato ranar farko ta watan Muharram, a matsayin hutu a jihar domin bai wa Musulmai dama su yi bukukunsu da addu’o’in sabuwar shekara cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

“Gwamnan Kwara, Malam AbdulRahman AbdulRazaq, yana taya al’ummar jihar, musamman Musulmai, murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 Hijira, yana masu fatan alheri da zaman lafiya.”

- Rafiu Ajakaye

Gwamna AbdulRazaq ya buƙaci al’ummar Musulmi da su yi nazari mai zurfi game da muhimmancin Hijira ga rayuwar al’umma da kuma zamantakewa a duniya baki ɗaya, rahoton Voice of Nigeria ya tabbatar.

Ya jaddada cewa Hijira ba kawai tarihi ba ne, illa tana ɗauke da darussa masu zurfi da za su taimaka wajen gina al’umma mai cike da zaman lafiya da fahimtar juna.

"Hijira tana koyar da mu sadaukar da kai, haƙuri da tawali’u domin ciyar da al’umma gaba. Tana nuna mana muhimmancin yin watsi da abubuwan da ke haddasa rikici, rashin zaman lafiya da rashin adalci a cikin al’umma."

Kara karanta wannan

Wike ya samu yadda yake so, PDP ta sanar da sahihin sakataren jam'iyya na ƙasa

- Rafiu Ajakaye

Gwamnatin Kwara ta ba da hutu
Gwamnatin Kwara ta ayyana Alhamis a matsayin ranar hutu Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Source: Twitter

Gwamnan Kwara ya yi kira ga jama'arsa

Gwamnan ya kuma yi kira da a ƙara ƙaimi wajen kyautata mu’amala da juna, zaman lafiya tsakanin ƙabilu da addinai daban-daban, da girmama juna cikin lumana da haƙuri.

Daga ƙarshe, Gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar cewa Allah ya sanya sabuwar shekarar Hijira ta zama ta alheri, wadata, tsaro, farin ciki mai ɗorewa da sabuntawar imani ga ɗaukacin al’ummar jihar Kwara da Najeriya baki daya.

A Najeriya ana samun wasu jihohin da suke ba da hutu idan sabuwar shekarar musulunci ta zagayo.

Tsohon gwamnan jihar Kwara ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga jimami a Kwara bayan samun labarin rasuwar tsohon gwamnan jihar, Cornelius Olatunji Adebayo.

Marigayin wanda kuma ya taɓa zama sanata ya yi bankwana da duniya ne yana da shekara 84 a ranar Laraba, 25 ga watan Yunin 2025.

Marigayi Cornelius Adebayo ya taɓa ƙin karɓar tayin minista a lokacin gwamnatin soja ta Janar Sani Abacha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng