'Abin da Ya Sa Maza Ke Kara Aure', Sheikh Ibrahim Khaleel
- Malamin addinin musulunci, Ibrahim Khalil ya taɓo batun dalilan da ya sanya maza suke jin ra'ayin ƙara aure a zukatansu
- A wajen wani taro da aka yi, Sheikh Ibrahim Khaleel ya bayyana cewa akwai mabambantan ɗalilai da suke sanya maza su ƙara aure
- Malamin ya kuma nuna cewa a yanayin tsarin halittar maza, babu wanda aka yi domin ya zauna da mace ɗaya a rayuwarsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Sheikh Ibrahim Khaleel ya yi magana kan dalilan da ya sa maza suke ƙara aure.
Malamin addinin musuluncin ya bayyana cewa maza na da mabambantan dalilai da suke sanya su ƙara aure.

Source: Facebook
Sheikh Ibrahim Khaleel ya yi jawabin ne a wajen wani taro na Matafiya Karaye da aka shirya wanda aka sanya bidiyon a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya bayyana cewa da yawan maza na ƙara aure ne saboda sha'awa, burgewa da burga.

Kara karanta wannan
Bayan yaƙi da Isra'ila, Shugaba Trump ya faɗi abin da Amurka za ta tunkari Iran da shi
Halayyar maza dangane da mata
Sheikh Ibrahim Khaleel ya bayyana cewa a yadda aka yi maza, an yi su ne don sha'awar mace ɗaya.
Ya ce babu wani namijin da yake sha'awar mace biyu.
"Idan doguwa ka ke so har abada doguwa kake so, idan gajeriya kake so har abada gajeriya kake so, idan sirirya ma haka.
"Amma wani dalili zai zo ya fizgeka, idan kana son doguwa za ka ga gajeriya ta fizgeka, wannan shi ne galibin aurukan da ake yi."
"Mafi yawan mutane za ka ga lokacin da za su yi aure wani abu ne ya fizgesu, kawai sun je sun ga ta basu sha'awa, ko ta burgesu, ko ta nuna tana sonsu ko kuma iyayensa ƴan uwansa mata, ba su son su gansa da mace ɗaya."
- Sheikh Ibrahim Khaleel
Maza na son ƙara aure
Sheikh Ibrahim Khaleel ya bayyana cewa an yi maza ne da son ƙara aure a zukatansu.

Source: Facebook
Ya ce duk namijin da yake da mace ɗaya to a zuciyarsa akwai son ta biyu.
"Duk namijin da ke da mace ɗaya to a zuciyarsa yana son ta biyu, wani dalili ne kawai ya hana shi."
"Idan ka tara maza 10, ɗaya ne kawai za ka samu a zuciyarsa baya son mace fiye da ɗaya.Amma shi ma ɗin da ka ga baya sha'awa, zai ce a zuciyarsa ai ni Allah don mace ɗaya ya yi ne, to idan ka bi a hankali tsoro da fargaba da gudun nauyi ne."
"Saboda haka duk wani namiji da ka gani da mace ɗaya ta wani dalili ne ya hana shi."
- Sheikh Ibrahim Khaleel
Matashi ya angwance da ƴar shekara 39
A wani labarin kuma, kuma kun ji cewa wani matashi mai suna Mustapha PK ya angwance da amaryarsa Anty Fati mai shekara 39 a duniya.
Mustapha PƘ ya bayyana cewa akwai soyayya mai ƙarfi a tsakaninsu duk kuwa da bambancin shekarun da suke da shi.
Ya bayyana cewa auren da ga ya yi ba a gina shi bisa son dukiya ko ƙwadayi ba domin shi ma yana da abin hannunsa.
Asali: Legit.ng
