Nasir El Rufai Ya Sake Dura kan Tinubu, Ya Yi Wa Ministocinsa Saukale
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya sake taso Shugaba Bola Tinubu a gaba kan ministocin da ya naɗa
- El-Rufai ya nuna cewa shugaban ƙasan ya naɗa mutane marasa inganci ne kawai a majalisar ministocinsa
- Ya bayyana cewa yana son gyara kuskuren da ya yi na taimakawa wajen samun nasarar shugaban ƙasan a zaɓen 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya soki mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a matsayin ministoci.
Malam Nasir El-Rufai ya bayyana majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu a matsayin wacce ba ta da masu inganci.

Source: Twitter
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da ake tattaunawa da shi a shirin 'Prime Time' na tashar Arise tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasir El-Rufai ya soki ministocin Bola Tinubu
Ya ce majalisar ba ta da ƙwarewar da ake buƙata don fuskantar ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.
El-Rufai ya ce ya yi tsammanin Tinubu zai maimaita tsarin shugabanci na ƙwararru da tafiya da kowa da ya yi a jihar Legas lokacin da yake gwamna daga 1999 zuwa 2007.
Sai dai ya bayyana rashin jin daɗinsa da yadda shugaban ƙasar ya tara majalisar ministoci mai yawan gaske amma marasa tasiri.
"Dubi majalisar ministocinsa abin dariya ne. Ita ce mafi yawa a tarihin Najeriya, kuma wataƙila mutum biyar kacal ne za a iya kiran su da sun cancanci zama ministoci."
"A lokacin da nake minista shekaru 20 da suka gabata, muna da mutane irinsu Ngozi Okonjo-Iweala da Oby Ezekwesili."
"Wa kake gani a wannan majalisa da ya kai irin wannan matsayi? Babu inganci ko kaɗan. Mun jefa Najeriya cikin masifa."
Tsohon gwamnan ya amince cewa yana ɗaya daga cikin masu laifi a wannan "masifa" da ya ce gwamnatin Tinubu ta jefa ƙasar nan a cikin ta.
Meyasa El-Rufai ya goyi bayan Tinubu a 2023?
Ya bayyana cewa goyon bayansa ga Tinubu a zaɓen 2023 ya samo asali ne daga abin da Tinubu ya cimma a Legas.

Source: Twitter
"Na mara masa baya ne saboda na yarda da abin da ya yi a Legas. Ya haɗa kowa. Ya ɗauko ƙwararru daga harkar kasuwanci irinsu Yemi Osinbajo da Wale Edun."
"Ya ba Igbo da Hausawa muƙamai masu muhimmanci, kuma abubuwa sun tafi daidai. Amma yanzu… me muke gani?"
"Ina jin alhaki ne a kaina na gyara wannan kuskuren. Ina da shekara 65 yanzu, ina dab da yin ritaya, amma ba zan iya hutawa ba sanin cewa na taimaka wajen kawo gwamnati da ke cutar da ƴan Najeriya."
"Zan yi duk mai yiwuwa, tare da wasu, mu dawo da lamarin bisa turba. Idan muka bari haka ba tare da an gyara ba, Najeriya za ta lalace."
- Nasir El-Rufai
El-Rufai ya faɗi dangantakarsa da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya taɓo batun dangantakar da ke tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ba shi da wata alaƙa a siyasance da shugaban ƙasan na Najeriya.
Tsohon gwamnan ya kuma nuna cewa Allah ya kare shi daga shan kunya ta hanyar hana shi shiga gwamnatin Tinubu.
Asali: Legit.ng

