Najeriya Ta Koma Mulkin Kama Karya na Farar Hula', Dele Momodu Ya Kawo Dalili
- Babban ƙusa a jam'iyyar adawa ta PDP, Dele Momodu ya nuna damuwa kan yadda dimokuraɗiyyar Najeriya ta taɓarɓare
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa yanzu ƙasar nan ta koma mulkin kama karya na farar hula
- Momodu ya koka kan yadda ƴan siyasa ke cin karensu babu babbaka ba tare da la'akari da halin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya bayyana cewa dimokiradiyyar Najeriya na cikin hatsari.
Dele Momodu ya bayyana cewa ƙasar nan tana komawa mulkin kama karya na farar hula.

Source: Facebook
Ya bayyana haka ne lokacin da ake tattaunawa da shi a shirin 'The Morning Brief' na tashar Channels Tv a ranar Laraba, 11 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Momodu ya ce kan dimokuraɗiyyar Najeriya?
Ya ƙara da cewa lamarin na da matuƙar baƙin ciki musamman ganin cewa ƙasar na shirin bikin ranar dimokuradiyya.
“Ina matuƙar farin ciki da cewa yau ta zo daidai da lokacin shirin bikin ranar dimokuradiyya, 12 ga watan Yuni. Saboda idan har akwai sauran ɗan ƙaramin tausayi a zuciyarmu, za mu gane cewa mun lalata wannan dimokuradiyya."
“A taƙaice, a jajibirin ranar 12 ga watanYuni, Najeriya ta dawo hannun shugabannin farar hula masu mulkin danniya waɗanda ba sa damuwa da yadda kake ji ko ra’ayinka. Ƴan Najeriya na cikin yunwa."
- Dele Momodu
Dele Momodu ya zargi jiga-jigan gwamnati da hukumomi da watsi da muradun jama’a, yana cewa shugabanni sun zama masu ƙarfi da rashin kunya a yadda suke mu’amala da ƴan ƙasa.
“Mun lalata wannan dimokuradiyya, kuma ina fatan ba mu lalata ta yadda ba za a iya gyarawa ba. Domin tsaurin idon da waɗannan ƴan siyasa suke da shi, ko a ɓangaren zartarwa, ko majalisa, ko ƙananan hukumomi, abin mamaki ne."

Kara karanta wannan
"Abubuwa sun lalace," Peter Obi ya faɗi hanya 1 da ƴan Najeriya za su ƙifar da Tinubu a 2027
- Dele Momodu

Source: Facebook
Dele Momodu ya ce an kunyata ƴan mazan jiya
Ya ƙara da cewa waɗanda suka yi gwagwarmaya kuma suka rasa rayukansu saboda dimokuradiyya a lokacin 12 ga watan Yuni, da sun ji matuƙar baƙin ciki idan suna raye a yau.
“Duk waɗanda suka wahala saboda wannan dimokuradiyya, musamman waɗanda yanzu suna lahira, idan da suna kallonmu, da hawaye sun riƙa zubowa daga idonsu."
- Dele Momodu
Dele Momodu ya faɗi hanyar kayar da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya ba ƴan adawa shawara kan zaɓen shekarar 2027.
Momodu ya bayyana cewa yin haɗaka ita ce hanyar da ƴan adawa za su bi domin kayar da shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam'iyyar a babban zaɓen 2027.
Jigon na PDP ya ƙara da cewa har yanzu jam'iyyar APC na PDP saboda ƙarfin da take da shi duk kuwa da irin rikicin da take fama da shi.
Asali: Legit.ng
