'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Farmaki Janar Buratai? An Ji Gaskiyar Zance
- Wasu kafafen yaɗa labarai sun yaɗa rahotannin da ke cewa an kai farmaki ga tsohon babban hafsan sojojin ƙasa,Tukur Yusuf Buratai
- Rahotannin sun bayyana cewa ana zargin ƴan ta'addan Boko Haram da kai harin kan Laftanan Janar Buratai mai ritaya
- An gudanar da bincike domin gano gaskiyar labarin wanda aka yaɗa a kafafen sada zumunta inda ake cewa Buratai ya tsallake rijiya da baya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - An yaɗa wasu rahotanni masu cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun farmaki tawagar tsohon babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) a Borno.
Rahotannin waɗanda aka yaɗa sun bayyana cewa Janar Tukur Yusuf Buratai ya kusa rasa ransa sakamakon wani kwanton bauna da ake zargin ƴan Boko Haram ne suka kai masa a jihar Borno.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, ya ƙaryata rahotannin a shafinsa na X.
Shin ƴan Boko Haram sun farmaki Janar Buratai?
An bayyana rahotannin a matsayin tsantsagwaron ƙarya ne da kuma yunƙurin ruɗar da jama’a.
Masanin ya tabbatar da cewa babu wani hari da aka kai wa tsohon babban hafsan sojojin ƙasan na Najeriya.
Hakazalika an sauya kalaman da Sanata Ali Ndume ya yi kan harin da ƴan Boko Haram suka kai a Buratai.
Wasu kafafen yaɗa labarai dai sun yaɗa labarin ba tare da wani tabbaci ko bincike ba, inda suke nuna cewa Ali Ndume ya ce an farmaki tawagar Tukur Buratai.
Abin da ya faru shi ne ƴan ta'addan ISWAP sun kai wani harin haɗin gwiwa inda suka kai farmaki a wurare uku daban-daban na sojoji a garin Buratai, ƙaramar hukumar Biu, a ranar Juma’a.
Hare-haren sun nufi hedikwatar bataliya, cibiyar zaman lafiya da magance rikici, da kuma makarantar sakandare ta sojoji, ba Janar Buratai ko wata motar rakiyarsa ba.
A bayyane yake cewa Laftanar Janar Buratai bai kasance a kusa da inda aka kai harin ba, kuma rayuwarsa ba ta kasance cikin haɗari ba.

Source: Original
Sojoji sun gwabza da ƴan Boko Haram
A lokacin harin, dakarun sojoji tare da goyon bayan jiragen yaƙi na Super Tucano na rundunar sojojin sama ta Najeriya, sun fatattaki ƴan ta’addan da ƙarfi da yaji.
A yayin fafatawar, an lalata motoci biyu na yaƙi da ISWAP ke amfani da su, kuma an kama ta uku a wani farmakin da aka kai daga baya.
An kashe ƴan ta’adda da dama, ciki har da fiye da 20 da jiragen yaƙi suka kashe yayin da suke tserewa ta hanyar Mangari.
Halin tsaro a Buratai yana karkashin kulawar jami’an tsaro, kuma dakaru na ci gaba da mamaye yankin domin hana wani sabon hari.
Ƴan Boko Haram sun kai farmaki a Buratai
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki kan wani sansanin sojojin da ke Buratai.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun ƙona kayayyakin aikin sojoji tare da sace wasu daga cikinsu a yayin harin.
Ya koka kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a jihar Borno tare da sauran wasu sassa na Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

