Gwamnatin Tarayya Ta ba da Hutu don Bikin Ranar Dimokuradiyya

Gwamnatin Tarayya Ta ba da Hutu don Bikin Ranar Dimokuradiyya

  • Gwamnatin tarayya ta fara shiry-shirye don bikin murnar zagayowar ranar dimokuraɗiyya a Najeriya
  • Ministan harkokin cikin gida ya ayyana ranar hutu a madadin gwamnatin tarayya domin zagayowar ranar dimokuraɗiyya
  • Olabunmi Tunji-Ojo ya ayyana ranar Alhamis, 12 ga watan Yunin 2025 a matsayin ranar hutu don murnar zagayowar lokacin bikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ba da hutu domin zagayowar ranar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni, 2025, a matsayin ranar hutu domin bikin ranar dimokuraɗiyya na bana.

Gwamnatin tarayya ta ba da hutun don ranar dimokuradiyya
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu don bikin dimokuradiyya Hoto: Hon. Olabunmi Tunji-Ojo
Source: Facebook

Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin tarayya ta ba da hutu

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr. Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Lahadi, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Halin da mahajjatan Najeriya 484 ke ciki bayan gobara ta kama otal ɗinsu a Makkah

A cikin sanarwar, ministan ya taya ƴan Najeriya murnar cika shekaru 26 na mulkin farar hula ba tare da yankewa ba.

Ya bayyana cewa ranar 12 ga watan Yuni tana da muhimmanci a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.

"Ranar 12 ga watan Yuni tana wakiltar muhimmin tarihi a tafiyarmu ta gina ƙasa mai adalci da gaskiya, inda zaman lafiya zai tabbata, kuma makomar al’umma ta kasance cikin tabbaci da kwanciyar hankali."

- Dr. Olabunmi Tunji-Ojo

Dr. Olabunmi Tunji-Ojo ya ƙara da cewa shekaru 26 da suka gabata sun nuna ƙarfin hali, juriya da jajircewar al’ummar Najeriya wajen riƙe aƙidar dimokuraɗiyya da fatan alheri da sabunta ƙwazo fiye da baya.

Minista ya nuna muhimmancin dimokuraɗiyya

Ministan ya bayyana cewa dimokuraɗiyya hanya ce da ake cigaba da inganta ta, ta hanyar ba da dama ga cigaba da sababbin sauye-sauye waɗanda za su kyautata rayuwar ƴan ƙasa.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu
Gwamnatin tarayya ta ayyana Alhamis a matsayin ranar hutu Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Ya bayyana cewa gwamnatin sabunta fata ƙarƙashin shugabancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana da cikakken niyya da ƙudirin ci gaba da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya na duniya.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojin Najeriya suka yi bikin sallah a fagen daga a Borno

Ya ce ƙa'idojin sun haɗa da amincewa da ikon jama’a wajen zaɓar shugabanninsu da kuma zaɓar hanyar siyasa, tattalin arziƙi, zamantakewa da al’adu da ƙasar za ta bi.

A ƙarshe, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan dimokuraɗiyya, su kare zaman lafiya da haɗin kai, da kuma ci gaba da sa hannu a ayyukan ci gaban ƙasa, domin tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da tafiya cikin nasara da ɗaukaka.

Gwamnatin Kano ta ba da hutu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ba da hutu domin jimamin hatsarin mota da ya ritsa da wasu ƴan wasan jihar.

Gwamnatin ta ba da hutun ne domin mutanen jihar su yi addu'o'i ga ƴan wasan waɗanda suka rasu sakamakon hatsarin motan da suka yi a kan hanyarsu ta dawowa gida.

Ƴan wasan dai sun wakilci jihar Kano ne a gasar wasanni ta ƙasa da aka gudanar a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng