Rufa Rufa Ta Ƙare, Gwamna Alia Ya Faɗi Jiga Jigai a Majalisa, Abuja da ke Taimaka wa Ƴan bindiga
- Gwamna Hyacinth Alia ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta gano manyan ƴan siyasa da ke da hannu a kashe-kashen da ake yi a Benuwai
- Alia ya ce akwai wasu ƴan siyasa a Majalisar Tarayya da Abuja, wandanda ke ba miyagu mafaka da saya masu kayan aiki
- Ya ce da zaran kwamitin da ya kafa ya gama aikinsa, gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace ba tare da duba girman mutum ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya zargi manyan 'yan siyasa da ke Abuja da Majalisar Tarayya da hannu a hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa jihar.
Gwamna Alia ya yi ikirarin cewa manyan ƴan siyasa ke ɗaukar nauyin miyagun ta hanyar ba su mafaka, ciyar da su da kuma samar masu da kayan aiki.

Kara karanta wannan
Gwamna Alia ya yi magana a ranar Sallah, ya bayyana yadda ƴan bindiga suka kewaye su

Source: Twitter
Hyacinth Alia ya yi wannan zargi ne a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin siyasa a yau na Channels TV a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu jiga-jigai ke taimakon ƴan bindiga?
Ya bayyana halin da jihar ke ciki da “abin damuwa matuka,” inda ya ce wadannan ‘yan siyasa suna fafutukar kare matsayinsu na siyasa ne, ba tare da la’akari da rayuwar al’umma ba.
“Abin damuwa ne matuka, domin manyan ‘yan siyasa da ke aiki a Majalisar Tarayya da Abuja su ne ke rura wutar matsalar tsaron Benuwai
"Ba suna haddasa rigima kaɗai ba ne, har suna bai wa wadannan miyagu mafaka, suna kula da bukatunsu a dazuka, suna ciyar da su da kuma sayo musu kayan aiki.
"Ba za mu lamunci wannan abu ba. Idan su ba su damu da rayuwar jama’a ba, muƙaminsu kaɗai suke son karewa, to ni kuma wakilin talakawa ne, kuma haƙƙi ne a kaina na kare su."
- Hyacinth Alia.
Gwamna Alia ya kafa kwamitin bincike
Duk da bai bayyana sunayen ‘yan siyasar da yake zargi ba, Gwamna Alia ya ce ya kafa wani kwamiti na bincike domin gano musabbabin hare-haren da ke jawo asarar gomman rayuwa.
Ya tabbatar da cewa a rahoton farko da kwamitin ya miƙa, ya gano manyan mutane da ke da hannu a lamarin, kamar yadda Punch ta rahoto.

Source: Original
“Mun kafa kwamitin bincike domin ya fayyace mana dalilin da yasa ake samun hare-hare daga cikin gida da waje.
"Mun riga mun karbi rahoton wucin gadi, kuma daga nan zuwa Talata ko Laraba na mako mai zuwa, zan karbi cikakken rahoto.”
"Da zarar mun karbi rahoton, za mu dauki matakin da ya dace. Sunayen mutane masu fada a ji sun fito fili a cikin rahoton, kuma zamu tunkari lamarin da muhimmanci.”
- Gwamna Alia.
Gwamna Alia ya gano tushen matsalar tsaro
A baya, kun ji cewa Gwamna Hyacinth Alia, ya bayyana cewa mugayen hare-hare da tashin hankali da ke faruwa a jihar Benuwai sun wuce rikicin manoma da makiyaya.
Mai Girma Alia ya kira halin da ake ciki a Benuwai da “ta’addanci” tare da bayyana cewa jihar tana kewaye da ƴan ta'adda.
Gwamnan ya ce abin ya fara ne da dan karamin sabani tsakanin makiyaya da manoma, yanzu ya rikide zuwa cikakken ta’addanci.
Asali: Legit.ng

