Gwamna Alia Ya Yi Magana a Ranar Sallah, Ya Bayyana Yadda Ƴan Bindiga Suka Kewaye Su
- Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana cewa hare-hare da kashe-kashen bayin Allah da ake yi a jihar Benuwai ya wuce faɗan manoma da makiyaya
- Mai girma Hyacinth Alia ya ce abubuwan da ke faruwa ba komai ba ne face ayyukan ta'addanci da wasu ƙungiyoyin ƴan bindiga ke aikatawa
- Gwamna Alia ya ce a yanzu jihar kewaye take da ƴan ta'adda, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa mugayen hare-hare da tashin hankali da ke faruwa a jihar sun wuce rikicin manoma da makiyaya.
Gwamna Alia ya kira halin da ake ciki a Benuwai da “ta’addanci” tare da bayyana cewa jihar tana kewaye da ƴan ta'adda.

Kara karanta wannan
Tsohon mawakin gargajiya a Najeriya ya rasu, Atiku da gwamna Mbah sun yi ta'aziyya

Source: Facebook
Hyacinth Alia ya faɗi haka ne a wani shiri na gidan talabijin na Channels TV ranar Juma’a, 6 ga watan Yuni, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Alia ya koka kan halin da Benue ke ciki
A cikin shirin, Gwamna Alia ya yi bayani mai cike da alhini game da zubar da jini da ake yi ba kakkautawa a wasu sassan jihar, musamman a yankin Sankera da Benuwai ta Yamma.
A cewarsa, a cikin makonni da suka wuce kadai, an kashe mutum 33 a sababbin hare-hare, yayin da a baya jihar ta yi rashin mutum 73 a wasu hare-hare da aka kai a kananan hukumomin Katsina-Ala, Ukum, da Logo.
"Bari in fayyace dalilin wadannan hare-hare. Matsalar tsaron da muke fama da ita yanzu ta samo asali ne tun shekaru da suka gabata.
"A wasu daga cikin wadannan kananan hukumomi, an dade da fuskantar wannan matsala fiye da shekaru 10. A Sankera, matsalar ta fi shekaru 16 zuwa 18,” in ji Gwamna Alia.
Yadda matsalar tsaro ta fara a jihar Benue
Gwamnan ya ce abin ya fara ne da dan karamin sabani tsakanin makiyaya da manoma, yanzu ya rikide zuwa cikakken ta’addanci, rahoton Daily Trust.
“A farko diyya kawai ake biya, idan an lalata gonar wani sai a biya diyya a kashe maganar, amma daga baya sai makiyaya suka fara zuwa da bindigogi irin su AK-47 da AK-49.
"Yanzu ma, ba makiyaya ke kawo hare-haren ba, ƙungiyoyin 'yan bindiga masu dauke da mugayen makamai ne ke zuwa, su kashe mutane, su kori al’umma daga gidajensu, su zauna a wurin,” in ji shi.

Source: Facebook
Wane mataki Gwamna Alia ya ɗauka?
Alia ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai da dama don tallafawa hukumomin tsaro, ciki har da siyan motocin Hilux 100 da wasu motoci 600 na sintiri don taimaka wa jami'an tsaro.
Gwamnan ya kuma yaba tare da miƙa godiya ga gwamnatin tarayya, wacce ya ce tana ƙoƙarin taimakawa jihar Benuwai a ƴan watannin da suka gabata.
“Lokacin da muka hau mulki, kananan hukumomi 17 ne ke cikin wannan rikici. Mun rage su zuwa tara, sannan zuwa shida. Amma cikin watanni biyu da suka gabata, lamarin ya kara tabarbarewa,” in ji shi.
Hafsan sojojin ƙasa ya koma Benue da zama
A wani labarin, kun ji cewa babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Oluyede, ya koma Makurdi domin jagorantar dakarun da za su dakile hare-haren ‘yan ta'adda a Benuwai.
An rahoto cewa Laftanar Janar Olufemi ya ɗauki wannan matakin ne sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga.
Oluyede zai gudanar da rangadi da kuma tsara yadda za a dakile hare-haren da gwamnatin jihar ta ce ana kai wa jama'a kusan kullum.
Asali: Legit.ng

