Neman Rigima: An Kira Dangote 'Shugaba' a Gaban Tinubu a Legas

Neman Rigima: An Kira Dangote 'Shugaba' a Gaban Tinubu a Legas

  • Aliko Dangote ya yi gyara da aka kirashi da “shugaba” a gaban shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wani taro da aka yi a jihar Legas
  • Dangote ya bayyana cewa a gaban shugaban ƙasa ba za a ce masa shugaban kamfani ba, har da yin barkwanci da neman gafara
  • Dangote ya bayyana sunan titin da ke kaiwa matatarsa da “Hanyar Bola Ahmed Tinubu” a matsayin girmamawa ga shugaban ƙasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lagos - Fitaccen ɗan kasuwan nan na Najeriya, Aliko Dangote, ya ja hankalin mai gabatar da taro (MC) bisa kuskuren kiransa da “Shugaba” a gaban shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, bayan kaddamar da titin shiga tashar jiragen ruwa na Lekki da ke Jihar Legas, wanda shugaban ƙasa ya gudanar.

Kara karanta wannan

"Tsarin Tinubu ya zo da alheri," An ji abin da ya jawo man fetur ya yi araha a Najeriya

Tinubu ya ziyarci matatar Dangote
Dangote ya yi martani bayan an kirashi da shugaba a gaban Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan yadda Bola Tinubu ya kaddamar da hanyar ne a cikin wani sako da Bayo Onanuga ya wallafa a X.

Dangote, cikin dariya da barkwanci, Dangote ya gyara kuskuren tare da roƙon gafarar Tinubu, yana mai cewa a bainar shugaban ƙasa bai kamata a kirashi da shugaba ba.

Dangote ya gyara kuskure da barkwanci

Yayin da ya fara bayani a taron bayan gabatar da shi, Dangote ya ce:

“Ya mai gabatarwa don Allah a nan gaba, idan shugaban ƙasa yana waje, sunana shi ne ‘jagoran kamfani’ ba ‘shugaba’ ba.”

Bayan gyaran kuskuren, Dangote ya juya ga shugaban ƙasa yana cewa:

“Ina ba da hakuri, ya kira ni shugaban kamfani. Ban yarda ya yi hakan ba, ranka ya daɗe.”

Dangote ya saka wa hanya sunan Tinubu

A yayin taron, Dangote ya sanar da cewa an saka wa titin da ke kaiwa zuwa Matatar Dangote suna “Hanyar Bola Ahmed Tinubu ” domin girmama shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya karɓi bakuncin fitaccen malami, Tunde Bakare, an ji abin da suka tattauna

Aliko Dangote ya ce wannan girmamawa ce ta musamman bisa irin rawar da shugaban ƙasar ke takawa.

Dangote ya karrama Bola Tinubu
An sa wa hanya sunan Tinubu a matatar Dangote. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dangote ya kara da cewa suna kashe Naira biliyan 900 wajen ayyukan raya kasa duk da sun biya haraji na biliyan 450 a bara.

Shugaba Tinubu ya kai ziyararsa ta farko zuwa Matatar Dangote, kafin daga bisani ya kaddamar da titin tashar jiragen ruwa ta Lekki da kuma wasu titunan a jihar Legas.

Fa'idar titin da Tinubu ya kaddamar

Sabon titi zai haɗa tashar jiragen ruwa, yankin kasuwanci na musamman da Matatar Dangote da babban titin Sagamu-Benin ta hanyar Ijebu Ode.

Masana sun bayyana cewa wannan titin zai taka rawar gani wajen sauƙaƙe zirga-zirgar kaya da ci gaban tattalin arziki a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Dangote ya yi magana kan farashin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci matatar Dangote da ke Lekki a jihar Legas.

A yayin ziyarar, Aliko Dangote ya bayyana cewa yana kara rage kudin litar fetur ne domin cinikin danyen mai da ake da Naira a Najeriya.

A kwanakin baya an samu tsaiko wajen cinikin danyen mai da Naira a Najeriya amma aka dawo bayan nada sababbin shugabannin NNPCL.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng