Malaman Jami'a Sun Shiga Kunci Saboda Rashin Biyansu Albashi a Sallah
- Farfesa daga ABU Zaria ya ce gwamnati na nuna rashin girmama malamai, musamman ma a lokacin bukukuwa kamar na Sallah
- Ya bayyana takaicin yadda ba a biya malamai albashin watan Mayu ba har zuwa rana ta 6 na watan Yuni ba tare da bayani ba
- Malamin jami'ar ya bayyana cewa rayuwa mai kyau ko sayen ragon sallah sun zama tarihi wajen malamai a Najeriya a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Wani sako mai sosa rai daga wani Farfesa a jami’ar Ahmadu Bello Zaria ya bayyana yadda malamai ke shiga kunci da takaici a lokacin sallah.
Farfesa Abdelghaffar Amoka ya wallafa sakon a ranar sallah, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a dandalin sada zumunta.

Source: Facebook
Legit ta tattaro maganganun da Farfesa Abdelghaffar Amoka ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, malaman jami'a a Najeriya na cikin mawuyacin hali, inda har zuwa rana ta shida a watan Yuni ba a biya su albashi ba.
Ya koka da cewa babban abin takaici ma shi ne suna zaune ba tare da wata hujja ko bayani daga gwamnatin tarayya ba.
Malaman jami'a na cigaba da kokawa ne adaidai lokacin da Musulmi ke gabatar bukukuwan Sallah a Najeriya.
Farfesa Amoka ya ce hakan na nuna yadda malamai suka zama marasa kima a idon gwamnati da al’umma baki ɗaya, inda ya bayyana cewa “wataƙila al’umma ba ta buƙatar malamai.”
Rayuwar malamai ta durƙushe inji Amoka
A cewar Amoka, sayen rago domin Sallah da ma gudanar da rayuwa mai kyau ya zama kamar mafarki ga malamai, inda ya nuna takaicinsa da cewa:
“Rayuwa mai inganci ba ta malami ba ce.”
Ya ce wani Farfesa ya nemi taimakon jama’a ta hanyar karo-karo domin biyan kuɗin magani, yayin da wani kuma ya fara sayar da tumatur da barkono domin ciyar da iyalinsa.

Kara karanta wannan
Musulmi zai iya cin bashi ya sayi ragon layya da Sallah? Babban limamin LASU ya yi bayani
Sai dai ya ce maimakon mutane su ji tausayinsu, sai suka dinga tafi da murna da cewa “ganin farfesa yana sana’a.”
A cewarsa, wannan lamari ba abin murna ba ne, illa nuna yadda tsarin ya gaza kare mutuncin malamai.

Source: Facebook
Amoka ya shawarci malaman jami'a
Farfesan ya jaddada cewa malamai suna ci gaba da sadaukar da kansu ga dalibai, duk da irin wulakanci da suke fuskanta, amma ya ce ya zama wajibi su duba lafiyar kansu da rayuwarsu.
Ya ce idan malami ya kamu da ciwo ko ya rasu, babu wani abin da za a iya yi masa face jimami na dan lokaci.
Ya jaddada cewa:
“Kada ka mutu saboda jami’a.”
Tinubu ya yi barka da sallah ga 'yan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya 'yan Najeriya murnar babbar sallah.
Shugaban kasar ya ce yana da tabbas a kan cewa komai zai tafi lafiya a Najeriya lura da cewa tsare tsarensa sun fara aiki.
Bola Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su tuna da mutanen karamar hukumar Mokwa da ambaliyar ruwa ta shafa a lokacin sallah.
Asali: Legit.ng
