Shiga Jirgi Kyauta: MURIC Ta Zargi Tinubu, NRC da Fifita Kiritoci kan Musulmi
- Kungiyar kare haƙƙin Musulmi, MURIC, ta zargi gwamnatin tarayya da nuna bambanci a harkar jigilar fasinjoji kyauta yayin bukukuwan addini
- MURIC ta ce gwamnatin ta ware Kiristoci da ba su damar hawa jirgin kasa kyauta a lokacin Kirsimeti, amma ba ta yi hakan ga Musulmi a lokacin sallah ba
- Ta yi kira da a duba tsarin hutun karshen mako da bukukuwan kasa da ta ce sun fi karkata ga Kiristanci tun daga zamanin mulkin mallaka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar kare haƙƙin Musulmi a Najeriya ta MURIC ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da jigilar fasinjoji kyauta yayin bukukuwan addini.
Kungiyar ta nuna rashin jin dadi ne tana mai zargin nuna wariya ga Musulmi a lokacin bikin sallah.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis yana caccakar gwamnatin da hukumar jirgin kasa na Najeriya (NRC).
Farfesan ya ce gwamnatin ta ba da damar hawa jirgi kyauta a lokacin Kirsimeti, amma ta yi shiru gaba ɗaya dangane da irin wannan damar a yayin bukukuwan sallah.
MURIC ta ce gwamnati ta ware Musulmi
A cewar Farfesa Akintola, hukumar NRC ta sanar da ƙarin zirga-zirgar jiragen kasa daga Legas zuwa Ibadan da sauran hanyoyi, amma kudi za a biya ba kyauta ba.
Shugaban kungiyar ya ce:
“Wannan ba zai kai ko kusa da abin da aka yi wa Kiristoci a lokacin Kirsimeti ba.”
MURIC ta ce hakan ya nuna cewa an ware Musulmi a cikin ƙasa da ke da shugaba Musulmi kuma da tikitin shugabanci na Musulm Musulm.
Farfesa Akintola ya yi tambaya da cewa:
“Shin jirgin kyauta na Kiristoci ne kawai?”
“Shin Musulmi suna cikin wannan gwamnati kuwa?”
The Guardian ta wallafa cewa kungiyar ta bayyana hakan a matsayin ci gaba da nuna wariya a fannin siyasa da tattalin arziki ga Musulmi.
MURIC ta fadi haka tana mai cewa tsarin hutun karshen mako da Najeriya ke bi na da tushe daga tsarin mulkin mallaka da ya fi karkata ga Kiristanci.
MURIC ta nemi a ba Musulmi haƙuri
A cikin sanarwar, MURIC ta nemi gwamnatin tarayya da ta ba da haƙuri idan abin da ya faru kuskure ne.
“Amma idan da gangan aka yi hakan, to wannan nuna iko ne da rashin adalci,”
Kungiyar ta kuma bukaci a sake nazari kan tsarin bukukuwa da hutun karshen mako domin tabbatar da adalci tsakanin Musulmi da Kiristoci a ƙasar.
MURIC ta roki Musulmi da su yi hakuri
Duk da wannan ƙorafi, MURIC ta taya Musulmi murnar Babbar Sallah da ke tafe, tana mai ƙarfafa su da su yi hakuri da juriya.

Source: Twitter
Shugaban MURIC ya ce:
“Ko da yake gwamnati da NRC ba su nuna adalci ga Musulmi ba, za mu ci gaba da hakuri. Muna da tabbacin cewa Allah mai adalci ne ko yaushe,”
NRC ta fitar da tsarin hawa jiragen kasa
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar jiragen kasan Najeriya ta NRC ta fitar da sanarwa kan yadda za ta yi aiki a lokacin sallah.
NRC ta bayyana cewa jiragen kasa da ke kan hanyar Kaduna-Abuja za zu yi aiki kamar yadda suka saba.
Baya ga haka, shugaban hukumar NRC ya taya Musulmai murnar babbar sallah yana mai cewa za su yi aiki yadda ya kamata.
Asali: Legit.ng


