Muhimman Abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Musulmin Najeriya da na duniya murnar bikin sallar layya na shekarar 2025
- Ya jaddada cewa bikin Sallah wata dama ce ta tunawa da sadaukarwa, biyayya da juriya kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna
- Shugaban ya ce Najeriyar na kan turbar farfaɗowa, inda ya roƙi ‘yan ƙasa da su dage da addu’a da haɗin kai don ciyar da ƙasa gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da saƙon taya murna ga al’ummar Musulmin Najeriya da na duniya dangane da shagulgulan bikin babbar sallah.
A cikin saƙon nasa, Tinubu ya bayyyana babbar sallah a matsayin wata dama ta musamman da ke ƙarfafa imani da sadaukarwa.

Kara karanta wannan
An kaɗa hantar Shugaba Tinubu kan matsalar tsaro, da yiwuwar a kifar da APC a zaben 2027

Source: Facebook
A sakon da Bayo Onanuga ya wallafa a X, Tinubu ya tunatar da al’umma muhimmancin biyayya ga Allah da ƙaunar juna a lokacin bikin sallah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran Tinubu ga jama'a kan bikin sallar layya
Tinubu ya ce babban darasin da bikin sallar layya ke koya wa al’umma shi ne sadaukarwa da cikakkiyar biyayya ga Allah, kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna a tarihi.
Ya buƙaci ‘yan Najeriya da su mayar da wannan lokacin na sallah tamkar wata sabuwar dama ta sabunta niyyar ƙaunar ƙasa, juriya da sadaukarwa domin cigaban al’umma gaba ɗaya.
Shugaban kasar ya ce:
“Idan muka fahimci ainihin ma’anar wannan biki, za mu samu kwarin gwiwa wajen ɗaukar matakan da za su ciyar da ƙasarmu gaba, domin makomar Najeriya na hannunmu.”
Tinubu: 'Najeriya na farfaɗowa daga matsin tattali'
Shugaban ya bayyana cewa, duk da cewa sauyi bai cika kasancewa cikin sauƙi ba, akwai alamun samun cigaba a bangaren tattalin arziki da zaman lafiya.

Kara karanta wannan
Musulmi za su yi Sallah cikin kwanciyar hankali, NSCDC ta ɗauki matakai a faɗin Najeriya
Shugaban ya ce an yi bankwana da kwanakin shan wahala kuma nan ba da jimawa ba ‘yan ƙasa za su fara jin sauyi a rayuwarsu.
Ya ce:
“Dukkan matakan da muka ɗauka suna fara haɓaka alamomin cigaba. Za mu cigaba da aiki ba tare da gajiyawa ba domin tabbatar da jin daɗin jama’a.”
Tinubu ya nanata cewa ajandar "Renewed Hope" za ta cigaba da kasancewa tubalin shirinsa na kawo sauyi a fannonin tattali, tsaro da walwalar al’umma, tare da tabbatar da adalci ga kowa.
Ya kuma bukaci 'yan Najeriya da kada su cire tsammnain samun sauki domin alamun shiga sabuwar rayuwa sun bayyana saboda tsare tsarensa.

Source: Facebook
Shugaban ya tuna da bala’in ambaliya da aka yi a Mokwa inda mutane suka rasa rayuka da dukiyoyi, yana mai roƙon da a rika addu’a da kuma ba da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.
Aminu Ado Bayero ya janye hawan sallah
A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Aminu Ado Bayero ya sanar da janye hawan sallah a jihar Kano.
Sarkin ya ce ya janye hawan sallah ne domin nuna goyon baya ga matakin da jami'an tsaro suka dauka a jihar.
Sai dai duk da haka, mai martaba Aminu Ado Bayero ya bukaci jama'a da kada su yi wasa da addu'ar zaman lafiya da cigaba.
Asali: Legit.ng
