'Yan Sanda Sun Yi Martani kan Batun Sace Mutane 200 a Hanyar Kaduna zuwa Abuja
- An yaɗa wasu rahotanni a kafafen sada zumunta masu cewa an sace mutane kusan 200 kan hanyar Ƙaduna zuwa Abuja
- Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta fito ta musanta rahotannin inda ta bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a cikinsu
- Hakazalika ta ƙara da cewa an kwashi shekara biyu ba tare da samun rahoton yin garkuwa da mutane ba a kan hanyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta yi martani kan rahoton da ke cewa an sace mutane 150 zuwa 200 a kan hanyar Abuja-Kaduna.
Rundunar ƴan sandan ta jihar Kaduna ta ƙaryata rahoton wanda ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ta ce babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna, Mansur Hassan ya fitar a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun musanta batun sace mutane
A cewar rundunar, rahoton tsantsagwaron ƙarya ce kawai da aka ƙirƙira, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Mansur Hassan ya ce ba a samu wani rahoton satar mutane a kan hanyar Abuja-Kaduna ba cikin shekaru biyu da suka wuce, sakamakon tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka a yankin.
Ya bayyana cewa yankin yana ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, tare da sintiri na yau da kullum daga ƴan sanda, sojoji, DSS da sauran hukumomin tsaro a jihar.
Jami’in ya ambato kwamishinan ƴan sanda na jihar yana gargaɗi ga mutane da kafafen yaɗa labarai da su daina yaɗa ƙarya, domin irin wannan na iya haddasa fargaba da tayar da tarzoma a cikin al’umma.
Mansur Hassan ya ƙara da cewa rundunar tana ɗaukar lamarin da muhimmanci, kuma za a iya gayyatar mutanen da suka yaɗa wannan ƙarya, ko kafafen da suka yaɗa ta, domin amsa tambayoyi da fuskantar hukunci.
Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da sauran hukumomin gwamnati na ci gaba da aiki tuƙuru don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ƴan sanda sun ba da shawara
Rundunar ƴan sandan ta roƙi jama’a da su riƙa dogara da sahihan bayanai daga hukumomin gwamnati kawai.

Source: Original
"Hankalin rundunar ƴan sanda ya kai kan wani rahoto mara tushe da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ‘Diaspora Digital Media’ ta wallafa, wanda ke cewa an sace mutane tsakanin 150 zuwa 200 a kan hanyar Abuja-Kaduna.”
"Rundunar tana sake jaddada cewa wannan rahoto ƙarya ne, ba shi da tushe ko makama."
"Domin fayyace gaskiya, ba a samu wani rahoton satar mutane a wannan hanya ba cikin shekaru biyu da suka wuce."
- Mansur Hassan
Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a wani wajen haƙar ma'adanai da ke jihar Kwara.
Ƴan bindigan sun hallaka wasu jami'an ƴan sanda guda biyu a yayin mummunan harin da suka kai.
Hakazalika sun kuma yi awon gaba da wani ɗan ƙasar China a harin da suka kai wurin haƙar ma'adanai da ke Oreke Oke-Igbo.
Asali: Legit.ng

