NRC Ta Yi wa Musulmai Gata wajen Hawa Jiragen Kasa a Lokacin Sallar Layya

NRC Ta Yi wa Musulmai Gata wajen Hawa Jiragen Kasa a Lokacin Sallar Layya

  • Yayin da bukukuwan Babbar Sallah ke ƙaratowa, Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ƙara wasu tafiye-tafiye don sauƙaƙa jigilar fasinjoji
  • Hukumar za ta yi jigilar fasinja a hanyar Lagos zuwa Ibadan da kuma daga Ibadan zuwa Lagos a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, 2025
  • NRC ta ƙaddamar da jigila ta musamman daga Warri zuwa Itakpe, domin bai wa Musulmi da sauran fasinjoji damar gudanar da tafiyarsu cikin sauƙi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta sanar da ƙarin jigilar jiragen ƙasa a wasu manyan hanyoyi yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Sallah.

Jami'in hukumar, Callistus Unyimadu ya bayyana cewa za a ƙara sababbin jigilar jiragen ƙasa daga Lagos zuwa Ibadan da kuma daga Ibadan zuwa Lagos a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

EFCC: Ƴan ƙasar waje sun ga takansu a Najeriya, ƙotu ta ɗaure su bayan kama su da laifi

NRC ta yi musulmai gata a lokacin sallah
An fitar da jadawalin jiragen kasa a lokacin sallah. Hoto: @info_NRC
Source: Twitter

Legit ta gano bayanan da hukumar ta yi ne a cikin wani sako da NRC ta wallafa a shafinta na X a ranar Laraba, 4 ga Yuni 2025.

Wannan mataki na daga cikin hanyoyin da hukumar ke bi wajen sauƙaƙa cunkoso da ake sa ran fuskanta a lokacin bukukuwan Sallah.

An bayyana cewa hakan zai kawo sauki wa jama'a, musamman ga Musulmai da ke shirin tafiya domin yin bukukuwan sallah tare da iyalansu.

Tsarin jigilar jirgin Legas-Ibadan yayin sallah

Hukumar NRC ta bayyana cewa za a samu karin tafiye-tafiye a hanyoyin Lagos zuwa Ibadan da Ibadan zuwa Lagos, domin ɗaukar yawan fasinjojin da ake sa ran za su fita a lokacin Sallah.

Sabon jadawalin ya nuna cewa jirgin Lagos zuwa Ibadan zai tashi da misalin ƙarfe 1:55 na rana, yayin da na Ibadan zuwa Lagos zai tashi da ƙarfe 11:03 na safe, a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Gwamna ya karrama jami'in NIS da ya ki karbar N10m wajen bokan da aka kama

Karin jigilar na da nufin rage cunkoso da kuma bai wa jama’a damar tafiya cikin sauƙi da kwanciyar hankali yayin da bukukuwa ke ƙaratowa.

Jirgin Warri-Itakpe zai yi aiki ranar Alhamis

Bayan Lagos-Ibadan, NRC ta bayyana cewa a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, 2025, jirgin Warri zuwa Itakpe zai yi aiki na musamman duk da cewa wannan rana a da an ware ta ne domin gyara.

An dage gyaran da ake yawan yi a ranar Alhamis zuwa ranar Lahadi, 8 ga Yuni, domin bai wa fasinjoji damar yin tafiya ba tare da tangarda ba a lokacin bukukuwan Sallah.

Har ila yau, hukumar ta ce jiragen Abuja zuwa Kaduna za su ci gaba da tafiya kamar yadda aka saba, tare da ƙarin wasu tsare tsare domin sauƙaƙa jigilar jama’a.

NRC ta taya Najeriya murnar sallah
NRC ta ce za ta yi aiki mai kyau da inganci a lokacin sallah. Hoto: @info_NRC
Source: Twitter

NRC ta taya Musulmai murnar Sallah

Shugaban hukumar NRC, Dr Kayode Opeifa, ya yi fatan alheri ga dukkan fasinjoji yayin wannan lokaci na bukukuwan Sallah.

Daily Trust ta wallafa cewa Dr. Kayode Opeifa ya ce za su tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Almajirai 11 sun rasu daga zuwa taimakon Malaminsu a jihar Kaduna

Aminu Ado ya janye hawan sallah a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Aminu Ado Bayero ya janye hawan sallah da aka saba yi a Kano duk shekara.

Fadar Aminu Ado Bayero ta ce ta janye hawan ne sakamakon bayanin da 'yan sanda suka yi da kuma hadarin 'yan wasan Kano.

Sarkin ya bukaci al'ummar jihar Kano su cigaba da addu'o'i domin tabbatar da zaman lafiya lura da yadda suke samun nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng