'Yan Kwadago Sun Yi wa Tinubu Wankin Babban Bargo bayan Cika Shekara 2 a Mulki

'Yan Kwadago Sun Yi wa Tinubu Wankin Babban Bargo bayan Cika Shekara 2 a Mulki

  • Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ce shekaru biyu da Bola Tinubu ya yi kan mulki sun jefa ma’aikata da talakawa cikin ƙarin wahala
  • NLC ta ce babu wani abin da za a iya murna da shi tun bayan da Tinubu ya hau mulki, face hauhawar farashi da ƙarancin abinci
  • Ƙungiyar kwadago ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da musgunawa shugabannin ƙwadago da watsi da alƙawuran da aka musu a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadagon Najeriya (NLC) ta caccaki gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa babu wani cigaba da talakawa suka samu tun bayan da ya hau mulki.

Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce shekaru biyu da suka gabata sun zo da yawaitar wahala, yunwa da durƙushewar tattali.

Kara karanta wannan

Minista ya kwarzanta gwamnatin Shugaba Tinubu, ya fadi tarihin da ta kafa

'Yan kwadago sun ce Tinubu ya gaza a shekara 2
'Yan kwadago sun ce matsaloli sun karu a mulkin Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Nigeria Labour Congress - HQ
Source: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa Ajaero ya ce Tinubu ya zo da alƙawarin sabuwar rayuwa, amma abin da kawowa saukar ga ‘yan Najeriya ita ce farfagandar siyasa da ɗaura musu wahalar rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: NLC ta ce farashin fetur ya tashi

NLC ta zargi gwamnatin Tinubu da ƙara jefa al’umma cikin wahala ta hanyar cire tallafin man fetur ba tare da wani shiri ba, abin da ya haifar da tashin farashi daga N187 zuwa sama da N600.

Ƙungiyar ta ce maimakon ganin amfanin cire tallafin, ‘yan Najeriya sun gamu da hauhawar farashi, rufe masana’antu da rage cin abinci a gidaje da dama.

NLC ta kuma bayyana cewa karyewar darajar Naira ta sa tattalin arzikin Najeriya ya yi kasa, inda masana’antu ke tagayyara sakamakon hauhawar farashin kayan da ake shigowa da su a ketare.

NLC ta nuna ma'aikata sun shiga damuwa

A cewar Joe Ajaero, gwamnati na cigaba da tauye haƙƙin ma’aikata da ƙungiyoyin ƙwadago ta hanyar tsoratarwa da rashin bin umarnin kotu kan albashi da hakkokin ma'aikata.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da wakilan gwamnati, ma'aikatan shari'a sun amince a janye yajin aiki

Ajaero ya bayyana cewa shirin samar da motocin CNG domin rage tsadar sufuri bai wadatar ba, sakamakon ƙarancin iskar gas da sauran matsalolin kayan aiki.

'Yan kwadago: 'Rashin tsaro ya karu a Najeriya'

A ra’ayinsa, ko da tsarin tattalin arziki zai yi tasiri, babu makawa sai an magance matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar kamar Boko Haram da masu garkuwa da mutane.

Ya ce rayuka da dukiyoyin al’umma na halaka kullum, yayin da gwamnati ke cigaba da tattaunawa marar tasiri kan tsarin kasafin kuɗi, alhali jama’a na fama da yunwa.

Yan kwadago sun ce matsalar tsaro ta karu a Najeriya.
'Yan kwadago sun ce Tinubu bai magance matsalar tsaro ba. Hoto: Bayo Onanuga|Nigeria Labour Congress - HQ
Source: Twitter

Bayanin Tinubu kan cika shekara 2 a mulki

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce ya samu nasarori bayan cika shekara biyu a karaga.

Bola Tinubu ya ce an samu saukar farashin kayayyaki a Najeriya sakamakon sauye sauye da gwamnatinsa ta yi.

Shugaban kasar ya ce an samu karin masu zuba jari zuwa Najeriya sakamakon tsare tsaren tallalin arkizi da ya yi a shekara biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng