"A Yi Hattara": Matashi Ya Bayyana Yadda Ya Tsira daga Hannun Masu Safarar Koda
- Wani matashi ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya a hannun masu safarar ƙoda da suka yi yunƙurin cutar da shi
- Sabi'u Usman Saurayi ya bayyana cewa masu safarar ƙoda sun yi yunƙurin cire masa ta shi amma Allah ya tseratar da shi
- Ya shawarci jama'a da su yi hattara tare da yin taka-tsan-tsan domin tabbas akwai masu sana'ar safarar ƙoda da ke yawo
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wani matashi mai suna Sabi'u Usman Saurayi, ya tuna baya kan yadda ya sha da ƙyar a hannun masu safarar ƙoda.
Sabi'u Usman Saurayi ya bayyana cewa an so a cire masa koɗa amma Allah bai nufa ba.

Source: Facebook
Matashin ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabiu Usman Saurayi ya bayyana cewa lamarin ya fara ne bayan da ya fara jin zazzaɓi a jikinsa.
Ya ƙara da cewa bayan ya ji zazzaɓin ya ƙi tafiya duk da maganin da ya sha, sai ya yanke shawarar zuwa asibiti idan gari ya waye.
An yi yunƙurin cirewa matashi ƙoda
Sabiu Usman ya bayyana cewa abubuwa sun ƙara dagule masa ne lokacin da yake tafiya kan babur tare da ɗan Achaɓa, inda ya ce ya ji cewa ba zai iya tafiya ba saboda jirin da yake ji.
"A lokacin da na zauna a bakin hanya, na ɗukar da kai ina jiran na farfaɗo sai na ji wani ya kira sunana, 'Sabiu me kake yi a nan?' Na kalli sama sai na ga wani mutum wanda ya nuna ya gane ni. Na gaya masa zan tafi asibitin Doma ne. Sai ya ce na zo ya rage min hanya."
"Ba tare da wani tunani ba, na shiga motarsa mai baƙin gilashi, saboda tarihin da na ke da shi na yin aiki a bankuna, ina haɗuwa da mutane sosai, ban ji wani abu ba kan ko ya sanni duk da cewa na kasa gane shi."
"Ban gane hatsarin da na shiga ciki ba, har sai da aka kulle ƙofofin da ke bayana. Nan da nan mutum biyun da ke bayana suka dawo da ni tsakiya, suka sanya min wani abu suka kulle min fuska."
"Mun yi tafiya ta kusan mintuna 25. Lokacin da aka cire min hular, sai na tsinci kai na a cikin wani ɗaki da bangane masa ba inda mutane uku suke zagaye da ni."
"Ɗaya daga cikinsu mai sanye da takunkumin fuska, ya buɗe wani ɗan akwati, ya ciro sirinji sannan ya ɗebi jinina. Ya kuma tilasta min na ba da samfurin miyau ta hanyar matsamin haƙarƙari, sannan ya buƙaci samfurin fitsari, na ce masa bana ji amma ya nace sai na ba shi."
"Ɗaya daga cikin mutanen wani dogo ƙato, ya buge ni sau biyu a baya. Duka da tsoron da na ji ya sanya na yi biyayya, na ba su samfurin."
"Sun ba ni abinci, amma na ƙi ci. Na tsorata kuma na shiga ruɗani kuma har yanzu ina jin zazzaɓi. Sai na hango agogon bango, lokacin ƙarfe 11:20 na safe."
"Sun bar ni a kulle a ɗakin, tun daga rana har zuwa dare sannan suka dawo wajen ƙarfe 10:00, ɗauke da abinci da ruwa. Amma na ƙi yarda na ci."
- Sabiu Usman Saurayi

Source: Facebook
Yadda matashin ya tsallake rijiya da baya
Ya ƙara da cewa ya fahimci cewa suna shirin tafiya da shi zuwa Kaduna don cire masa ƙoda, da nufin sayar da ita a kasuwa.
Ya bayyana cewa bayan ya fahimci hakan, sai ya fara nema hanyar da zai samu ya tsere.
Matashin ya bayyana cewa da ƙyar ya samu ya tsere ta cikin silin inda ya bi ta cikin rufin ɗakunan.
Ya bayyana cewa ya ba da labarin ne domin ya sanar da mutane cewa safarar koɗa da gaske ana yinta, kuma ya kamata jama'a su yi hattara.
Mata ta gutsurewa masoyinta mazakuta
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mata ta shiga hannun ƴan sanda bayan ta cirewa masoyinta mazakuta.
Rundunar ƴan sandan ta cafke ƴar shekara 43 mai suna Gift bisa zargin aikata hakan ne yayin rigima da saurayinta a Diobu da ke jihar Rivers.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku ne bayan saurayin matar ya nemi su shiga daga ciki su sadu da juna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


