Sallah: Gwamnatin Kano Ta Hango Matsala, Ta Gargaɗi Musulmi kan Dabbobin Layya
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ja hankalin mutanen jihar Kano kan dabbobin da za su yanka domin layya a lokacin babbar sallah
- Kwamishinan lafiya na Kano, Abubakar Labaran ya bukaci jama'a su yi taka tsan-tsan, su tabbatar da lafiyar dabbobin da za su yanka
- Ya taya ɗaukacin al'ummar musulmi na Kano murnar zagayowar sallah tare da fatan za su yi shagali cikin kwanciyar hankali da lumana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta gargaɗi mutane game da dabbobin da za su yi layya da su a babbar sallah.
Gwamnatin ta bukaci mazauna jihar da su tabbata dabbobin da za su yanka a lokacin Sallar Layya mai zuwa lafiyayyu ne da za a iya ci.

Source: Getty Images
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya, Nablusi Ahmad, ya fitar a ranar Laraba a Kano, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan
Gwamna Bago ya bi sahun ƴan sandan Kano, ya hana hawan Sallah saboda abin da ya faru
Ya ce kwamishinan lafiya, Abubakar Labaran, ne ya yi wannan gargaɗin yayin da musulmai ke shirye-shiryen bukukuwan babbar sallah nan da ƴan kwanaki.
Gwamnatin Kano ta bada shawarar kula da lafiya
Kwamishinan ya ce hakan zai taimaka wajen kare lafiyar jama’a da kuma dakile yaduwar cututtukan da mutane ke iya ɗauka daga dabbobi.
Abubakar Labaran ya yi gargadi cewa akwai wasu cututtuka da ke iya yaduwa daga dabbobi zuwa mutane, musamman idan ba a dafa nama yadda ya kamata ba.
"Ya kamata mutane su ba da muhimmanci matuƙa wajen yadda ake dafa naman. Dafa shi sosai yana taimakawa wajen kashe ƙwayoyin cuta da ke tattare da dabbobin,” in ji shi.
An buƙaci ƴan Kano su tsaftace naman layya
Kwamishinan ya kuma bukaci iyaye mata da masu girki da su kula da tsaftar nama da kayan abinci yayin girki domin hana kamuwa da cututtuka.
Labaran ya shawarci jama’a da su wanke nama sosai da tsaftataccen ruwa kafin a dafa ko a adana shi.
Abubakar Labaran ya tabbatar da cewa gwamnati na da isassun magunguna da kayan agaji a cibiyoyin lafiya domin ba da kulawa cikin gaggawa idan an samu matsala.

Source: Facebook
Ya kuma jaddada cewa ma’aikatar lafiyar ta jihar Kano ta kuduri aniyar ci gaba da kare lafiyar jama’a ta hanyar dakile yaduwar cututtuka, rahoton Guardian.
A karshe, kwamishinan ya taya jama’ar jihar Kano murnar zagayowar Sallah, tare da yi musu fatan za su gudanar da shagulgula cikin kwanciyar hankali, zaman lafiya da farin ciki.
'Yan sanda sun haramta hawan sallah a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar ‘Yan Sandan Kano ta sake jaddada haramcin gudanar da hawan Sallah a fadin jihar yayin bukukuwan babbar sallah.
Wannan mataki da ƴan sanda suka sake ɗauka ya saɓa wa mai martaba, Muhammadu Sanusi II, wanda ya fara shirye-shiryen hawan sallah.
Rundunar ƴan sanda ta taya musulmi da mazauna jihar Kano murnar zagayowar babbar Sallah, tare da kira da a kiyaye doka da oda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
