Hankulan Jama'a Sun Kwanta da 'Dan Bindiga Ya Mutu a Asibiti yayin da Yake Jinya
- Wani dan bindiga da ake zargi, Abu Alhaji, ya rasu a asibiti bayan kama shi a Katsina-Ala da ke Benue, ranar 1 ga Yunin 2025
- Rundunar tsaro ta cafke shi da AK-47 dauke da harsasai 16, yayin da wasu mutum 10 da ake zargi da hannu aka tsare a Makurdi
- Abu Alhaji ya fara jin jiki a ranar 3 ga Yuni, aka garzaya da shi asibiti inda ya mutu, ana ci gaba da binciken sauran yan bindiga da aka kama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Kwanan wani ɗan bindiga da ya addabi al'umma ya zo ƙarshe a jihar Benue da ake fama da kashe-kashe.
Ɗan bindigar da ake zargi, Abu Alhaji, wanda aka kama a yayin wani samame a karamar hukumar Katsina-Ala, ya rasu.

Kara karanta wannan
Ta'addanci: Jagororin Fulani sun nemi a tattauna, an sako Turji cikin masu neman sulhu

Source: Twitter
Rikakken dan bindiga ya mutu a asibiti
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa dan ta'addan ya mutu ne a asibitin koyarwa da ke Makurdi a jihar Benue.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun tattaro cewa an kama mamacin ne a ranar 1 ga Yuni, bayan samun bayanan sirri game da wasu ‘yan bindiga.
Ana zargin suna aiki da shugaban gungun wasu yan ta'adda, Amakaa Akwaza, wanda aka fi sani da “Konyo,” a wani maboya da ke Nagu, Katsina-Ala.
"Da misalin karfe 11:40 na safe, jami’an tsaro suka samu bayanan sirri, suka je wurin, suka fafata da ‘yan bindigar a arangama mai zafi.
"Wani Abu Alhaji ‘namiji’ wanda aka yi nasara a kansa, an kama shi da bindigar AK-47 mai dauke da harsasai 16.
"An kuma kama wasu mutum 10 da ake zargi suna aiki da gungun Konyo wajen ta da zaune tsaye a yankin Sankera, aka tsare su a cibiyar tsarewa ta Operation Zenda da ke Makurdi."
- Cewar wata majiya

Source: Original
Jami'an tsaro na binciken sauran yan bindiga
Sai dai majiyoyin ‘yan sanda sun ce da misalin karfe 3:05 na asuba ranar 3 ga Yunin 2025 da muke ciki ne aka ɗauki dan bindigar zuwa asibiti.
An ce Abu Alhaji ya fara jin jiki, aka garzaya da shi asibitin koyarwa na jihar Benue, inda ya rasu yana karbar magani.
An ajiye gawarsa a dakin ajiye gawawwaki na asibitin domin gudanar da binciken likitoci da kuma sanin matakin da za a dauka a gaba.
Majiyoyin sun kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan ayyukan sauran wadanda aka kama yayin samamen.
Matsalar 'yan bindiga a Arewa
Arewacin Najeriya na fama da mummunan koma baya sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da ke ta da zaune tsaye, hallaka mutane da raunata rayuwar yara da mata.
Wadanda ke cikin wannan ta’asa ba sa kallon kowa da daraja, sun addabi kauyuka da birane, suna kisan gilla, satar mutane da barna.
Lamarin ya kai ga mutuwar yara kanana da kuma jefa iyaye cikin bakin ciki da radadi. Yara da ya kamata su kasance a makaranta, yanzu sun koma gudu cikin dazuka, wasu kuma sun rasa iyayensu sakamakon harin da ‘yan ta’addan ke kaiwa.
Duk da nasarorin da jami’an tsaro ke samu, kamar yadda aka kama Abu Alhaji da wasu abokan aikinsa a Katsina-Ala, har yanzu akwai bukatar ƙara azama da dabaru wajen murkushe wannan barna.
Mutuwar Abu Alhaji ba karamin sauki ba ce ga al’umma, amma akwai sauran rina a kaba. Har yanzu gungun Konyo da sauran miyagun kungiyoyi na nan suna yi wa mutane barazana.
Idan ba a dauki mataki da gaggawa ba, Arewa za ta cigaba da zub da jini, da rasa matasa da yara waɗanda su ne ginshikin gobe. Gwamnati da al’umma su hada kai wajen ceton yankin.
Hafsan sojoji ya koma Benue da zama
A wani labarin, kun ji cewa Hafsan sojin Najeriya, Laftanar-Janar Oluyede, ya koma Makurdi domin jagorantar dakarun da za su dakile hare-haren ‘yan ta'adda.
Majiyoyi sun nuna cewa an kashe fiye da mutum 300 cikin watanni biyu a Benue, inda aka kona gidaje da korar jama’a daga kauyukansu yayin hare-haren.
Oluyede zai duba sansanonin soji kuma ya gana da jami’ai da jama’ar kauyauka, domin ƙarfafa gwiwar sojoji da tabbatar da tsaro a fadin jihar baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

