Bawa: An Fara Jin Yadda Aka 'Sace' Kuɗin Tallafin Fetur, Tsohon Shugaban EFCC Ya Saki Littafi
- Tsohon shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ya rubuta littafi kan yadda aka wawure kuɗin tallafin man fetur a Najeriya
- Bawa ya rike hukumar yaki da rashawa ta ƙasa watau EFCC daga watan Fabrairu, 2021 zuwa watan Yuni, 2023
- Littafin dai ya tona asirin hanyoyin da jami'an gwamnati da ƴan kasuwa ke bi wajen wawure kuɗin tallafin mai a ƙasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya kaddamar da sabon littafi game da badaƙalar tallafin man fetur.
Littafin da Bawa ya rubuta ya yi bayani dalla-dalla kan yadda aka sace tare da wawure kudade da sunan tsarin tallafin man fetur a Najeriya.

Source: UGC
Jaridar The Cable ta tattaro cewa tsohon shugaban EFCC ya raɗawa littafin suna, “The Shadow of Loot & Losses: Uncovering Nigeria’s Petroleum Subsidy Fraud,” kuma ya kunshi batun tallafin mai.
Yaushe za a fitar da littafin tsohon shugaban EFCC?
Za a fitar da wannnan littafi a hukumance a ranar 5 ga Yuni, 2025, karkashin Cable Books, wani sashe a kamfanin Cable Media and Publishing Ltd.
Haka nan kuma za a rika sayar da littafin a fadin Najeriya ta hannun shagon sayar da litattafai na Roving Heights Bookstore.
Bawa ya rike kujerar shugaban EFCC daga Fabrairu 2021 zuwa Yuni 2023, lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda Guardian ta rahoto.
Kafin ya zama shugaban EFCC, Bawa ya kasance daya daga cikin manyan masu bincike a kwamitin musamman da EFCC ta kafa domin binciken badakalar tallafin man da ta kunno kai a shekarar 2012.
Abubuwan da littafin Abdulrasheed Bawa ya ƙunsa
A cikin littafin, Bawa ya bayyana yadda aka wawure biliyoyin Nairori ta hanyar dabaru da dama kamar:
- Shigo da kaya na bogi
- Karin kudin da babu cikakken bayani a kansu
- Maimaita karbar tallafi
- Canja takardun shigo da kaya
- Safarar mai zuwa kasashen waje

Source: Twitter
Tsohon shugaban EFCC ya kara da cewa an yi amfani da waɗannan dabaru ne ta hanyar takardun bogi, rashin kulawa da haɗa baki tsakanin jami'an gwamnati da ƴan kasuwa.
Bawa ya tona yadda aka sace kudin tallafi
A cewarsa, littafin ba kawai tona badaƙalar cin hanci da rashawa kaɗai ya yi ba, ya ankarar da mahukunta domin daukar mataki da kuma riko da gaskiya a harkar tafiyar da kudaden jama’a a Najeriya.
A ranar 29 ga Mayu, 2023, lokacin rantsar da shi, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da tuge tallafin man fetur.
Daga nan, farashin man fetur ya tashi daga N190 zuwa N500, har ya haura N1,000 kafin ya ɗan fara saukowa, wanda ya yanzu ake sayarwa kan N850 ko sama da haka.
EFCC ta yi nasiha da hadinin Manzon Allah SAW
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta yi jan hankali kan cin hanci da rashawa ta hanyar amfani da hadisin Manzon Allah (SAW).
EFCC ta yi amfani da hadisin Sahih Muslim wanda ya yi gargadi kan almundahana da kuma abin da zai biyo baya, idan shugaba ya wawuri dukiyar talakawa.
Hadisin ya gargadi shugabanni da su guji boye ko satar dukiyar jama'a, yana cewa za su zo da ita a ranar lahira duk yawanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


