"Ban Cacar Baki da Yara": Amaechi Ya Yi Wa Nyesom Wike Wankin Babban Bargo

"Ban Cacar Baki da Yara": Amaechi Ya Yi Wa Nyesom Wike Wankin Babban Bargo

  • Rotimi Amaechi ya kasa kawar da kai kan kalaman da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi a kansa
  • Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana cewa yana matsayin ubangidan Nyesom Wike domin shi ne ya ɗauke shi aiki
  • Rotimi Amaechi wanda ya yi minista a mulkin APC ya ce ba zai ƙasƙantar da kansa ba ta hanyar yin cacar baki da yara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi martani kan kalaman da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi a kansa.

Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ba zai maida kansa yaro ba wajen yin cacar baki da Nyesom Wike.

Rotimi Amaechi ya caccaki Nyesom Wike
Amaechi ya yi wa Nyesom Wike tonon silili Hoto: @ChibuikeAmaechi, @GovWike
Source: Twitter

Tsohon ministan sufurin ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar talabijin ta Arise Tv a ranar Talata, 3 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan

Sabon rikici: Wike ya kwatanta Gwamna Fubara da 'dan da ya gujewa ubansa

Amaechi ya bayyana cewa Wike ya taɓa kasancewa shugaban ma’aikatan fadar gwamnatinsa, don haka yana ƙasa da shi a siyasance.

Nyesom Wike ya caccaki kalaman Amaechi

A lokacin bikin cikarsa shekaru 60 makon da ya gabata, Amaechi ya bayyana cewa kamar yadda miliyoyin ƴan Najeriya ke fama da yunwa, shi ma haka yake fama da ita.

Sai dai Wike ya yi watsi da kalaman Amaechi, yana mai cewa kalamansa wata dabara ce kawai don neman samun muhimmanci a siyasa.

Wike ya ce ba yunwar abinci Amaechi ke ji ba, yunwar neman samun mulki ne.

A shekarar 2021, Wike ya ce shi ne ya sa Amaechi ya zama gwamna a zaben 2007, a lokacin da shi ya tafi kasar Ghana.

Wane martani Amaechi ya yi wa Wike?

Amma Amaechi ya musanta wannan ikirari, inda ya bayyana cewa ko kaɗan ba haka zancen yake ba.

"Allah, Peter Odili, ɓangaren shari'a, da kuma mutanen jihar Rivers ne suka sa na zama gwamna."

Kara karanta wannan

Bayan ragrgazar gwamnatin APC, Amaechi ya dura kan shugaban INEC

"Ka tambaye shi yadda ya ce ya sa ni na zama gwamna. Ina faɗin haka ne saboda bana son shiga cacar baki da yara."
"Na taɓa zama ubangidansa. Ko yana so ko baya so. Ni na ɗauke shi aiki. Da na ce a'a, ba zai samu ba."

- Rotimi Amaechi

Wike da Amaechi sun yi cacar baki
Amaechi ya bayyana cewa shi ubangidan Wike ne Hoto: @GovWike, @ChibuikeAmaechi
Source: Facebook

Amaechi ya ce Wike yaronsa ne a siyasa

Amaechi ya ce ya naɗa Wike a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati maimakon kwamishinan kuɗi ne domin ya riƙa kula da shi sosai.

"Na zaɓe shi shugaban ma’aikata ne saboda na riƙa sa ido a kansa. Ban ba shi matsayin kwamishinan kuɗi ba. Ka ga, ina faɗin haka ne saboda bana son shiga gardama da yara."
"Ka ga shi ne ya sa kansa shugaban ma’aikata. Ya sa kansa Gwamna. Ya sa kansa Minista. Ya sa kansa shugaban ƙaramar hukuma."

- Rotimi Amaechi

Rikicin Wike da sauran 'yan siyasa

Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, na fuskantar sabani da dama da ‘yan siyasa a Najeriya, har ma da na jam’iyyarsa ta PDP.

Wike ya dade yana dabaibaye da rikice-rikice da manyan ‘yan siyasa tun bayan da ya bar kujerar gwamna a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

'Wike ya fara nuna alamun zagin Tinubu,' Abati ya gargadi shugaban kasa

Rikicinsa da Rotimi Amaechi ba sabon abu ba ne, amma yanzu yana kara ta’azzara, inda kowannensu ke kallon ɗan uwansa a matsayin ƙarami a siyasa.

Sauran abokan rikicin Nyesom Wike

Baya ga Amaechi, Wike na fama da rashin jituwa da wasu jiga-jigan PDP, musamman bayan rikicin zaben fidda gwanin shugaban kasa a 2022, wanda ya sa ya ki goyon bayan dan takarar jam’iyyarsu, Atiku Abubakar.

Hakan ya janyo rabuwar kai tsakanin shi da sauran shugabannin PDP da ke ganin yana cin karo da manufofin jam’iyya.

A yanzu, wasu na kallon Wike a matsayin dan siyasa mai son yin mulki da iko ko ta wace hanya, inda ke amfani da mukaminsa na minista wajen fito-na-fito da abokan adawa, da ma na gida.

Sabani da Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya sake bayyana irin wannan halin, inda har ya kai ga rabuwar kawunan gwamnati da masu ruwa da tsaki. Wannan hali yana barazana ga zaman lafiya da daidaituwar siyasar Najeriya.

Rotimi Amaechi ya caccaki shugaban INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya soki shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan APC na shirin ficewa jam'iyyar? An ji gaskiyar zance

Amaechi ya bayyana cewa da a ce Mahmood Yakubu ne shugaban INEC a 2015, da jam'iyyar APC ba ta samu nasara ba.

Tsohon gwamnan ya zargi shugaban na hukumar INEC da nuna ɓangaranci da son kai a wajen gudanar da ayyukansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng