Jirgin Ruwa Ya Kife da Mutane a tsakiyar Kogi a Sokoto, an Rasa Rayuka
- Rahotanni daga hukumar NEMA sun tabbatar da hatsarin kwale-kwale a kauyen Sullubawa da ke ƙaramar hukumar Shagari a jihar Sokoto
- Mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a cikin hatsarin da ya auku da safiyar Litinin, 2 ga Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 9:30 na safe
- Rahotannin farko sun nuna iska mai ƙarfi ce ta haddasa kifewar kwale-kwalen a tsakiyar kogin da mutane suke wucewa ta cikinsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa an yi wani mummunan hatsarin kwale-kwale a Sokoto.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hadarin ya auku ne a ƙauyen Sullubawa, wanda ke cikin ƙaramar hukumar Shagari ta jihar Sokoto.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan hadarin ne a cikin wani sako da hukumar NEMA ta wallafa a shafinta na X a ranar Laraba.
Wannan mummunan lamari ya faru ne da safiyar Litinin, 2 ga watan Yuni, inda kwale-kwalen da ke ɗauke da mutane ya kife a tsakiyar kogi, yana mai sanadin mutuwar mutum bakwai.
Haɗin gwiwar jami’an NEMA da hukumar agajin gaggawa ta jihar Sokoto (SEMA) ya isa yankin domin tattara bayanai kai-tsaye daga wurin da abin ya faru.
Dalilin hadarin jirgin ruwa a Sokoto
Rahotanni daga tawagar hadin gwiwar sun nuna cewa iskar da ta taso da ƙarfi ce ta haddasa kifewar kwale-kwale yayin da yake tafiya a tsakiyar kogin yankin Sullubawa.
Wannan hatsari ya sake jaddada matsalolin da ke tattare da tafiya a ruwa, musamman a lokacin damina, inda kwale-kwale ke yawan fuskantar haɗari sakamakon yanayin ruwa da iska.
Tawagar jami’an agaji ta hadu da shugaban ƙaramar hukumar Shagari da kuma ɗan majalisa mai wakiltar yankin, inda suka bayyana alhini da jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwa.
NEMA da SEMA sun fara bincike a Sokoto
Jami’an NEMA da SEMA sun bayyana cewa suna ci gaba da bincike domin tabbatar da ainihin musabbabin hatsarin.
Baya ga haka, za a zurfafa bincike domin a gano matakan da za a ɗauka domin hana faruwar irin haka a nan gaba.

Source: Twitter
A cewar hukumar, ana sa ran za a gudanar da wayar da kan al’umma kan matakan kare kai yayin zirga-zirga ta ruwa, tare da duba yiwuwar samar da rigunan kariya da dokokin tafiya a ruwa.
A halin yanzu dai, hukumomin suna ci gaba da kula da lafiyar wadanda suka tsira da kuma ɗaukar matakin tabbatar da cewa irin wannan musiba ba ta sake faruwa ba a yankin.
An yi hadarin jirgin ruwa a Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa an samu mummunan hadarin jirgin ruwa a wani yanki na Arewacin jihar Kwara a kwanakin baya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu hadarin ne a Gbajibo, karamar hukumar Kaiama sakamakon iska mai karfi.
Legit ta rahoto cewa shugaban karamar hukumar Kaiama ya ce gwamnati za ta dauki matakai masu tsauri kan tafiya a ruwa da dare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

