Bayan Ragargazar Gwamnatin APC, Amaechi Ya Dura kan Shugaban INEC
- Tsohon ministan sufuri a gwamnatin Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi ya yi kaca-kaca da shugaban hukumar zaɓe ta INEC
- Amaechi ya bayyana cewa da ace Farfesa Mahmood Yakubu ne shugaban INEC a. 2015, da jam'iyyar APC ba ta kai labari ba a zaɓen
- Tsohon gwamnan ya kuma ƙwararo yabo ga tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, kan yadda ya yi aiki mai kyau a hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya soki shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na yanzu, Farfesa Mahmood Yakubu.
Rotimi Amaechi ya zargi cewa da shi ne shugaban hukumar a lokacin zaɓen 2015, da jam’iyyar APC ba za ta samu rajista ba, kuma ba za ta yi nasara a zaɓen ba.

Source: Twitter
Tsohon ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tv da yammacin ranar Talata, 3 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amaechi ya yabawa Attahiru Jega
Rotimi Amaechi ya yabawa tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, saboda tabbatar da tsarin zaɓe mai gaskiya da adalci wanda ya haifar da rajistar APC da kuma nasararta a zaɓen shekarar 2015.
"Shugaban INEC na yanzu, idan da shi ne shugaban INEC a 2015, da ba mu ci zaɓe ba. Wannan magana ce mai muhimmanci."
"Allah ya saka wa Jega da alheri, domin ƙa’idojin zaɓe sun kasance a bayyane. Shugaban INEC na yanzu za a iya haɗa shi ne kawai da Iwu."
“Lokacin da muke son rajistar APC, Jega ya buɗe ƙofa, muka bi dukkan sharuddan rajista. Shi ne ya tabbatar da rajistar APC. Wanda ke kan kujerar a yanzu, ko da ka cika duk waɗannan sharudda, ba zai maka rajista ba."
- Rotimi Amaechi
INEC: Amaechi ya soki shugaban hukumar zabe
Amaechi ya ƙara da cewa INEC ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu na nuna son kai tun yanzu.

Source: Facebook
“Tun yanzu INEC na nuna ɓangaranci. Abin da zan iya faɗa yanzu shi ne, idan ka duba yadda Najeriya ke gudanar da zaɓe, ko tsarin yin amfani da A4 ya fi ci gaba."
"Aƙalla, akwai gaskiya da bayyananniyar hanya. Kana ganin komai a fili. Daga baya sai muka dawo muka tarar da mutane irin su Iwu da sauransu, har da wanda ke kai yanzu, abubuwa suka ƙara lalacewa."
“Don haka, ba ka san ko za ka ce muna gaba ko muna baya ba. Akwai wani irin ƙoƙarin mallakar ƙasa ta hanyar amfani da hukumar zaɓe."
- Rotimi Amaechi
Menene Amaechi ya faɗawa Tinubu a 2023?
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi nagana kan yadda ta kaya tsakaninsa da Bola Tinubu, gabanin zaɓen 2023.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ya gayawa Tinubu cewa ba zai mara masa baya ba, kuma ba zai zaɓe shi ba a takarar 2023.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda ya yi amanna cewa Tinubu bai da ƙwarewar da zai shugabanci Najeriya.
Asali: Legit.ng

