Minista Ya Kwarzanta Gwamnatin Shugaba Tinubu, Ya Fadi Tarihin da Ta Kafa
- Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya kwararo yabo ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Alhaji Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta yi wa waɗanda suka gabace ta nisa nesa ba kusa ba
- Ministan ya nuna cewa gwamnatin ta samu nasarori waɗanda gwamnatocin baya ba su same su ba a cikin shekara biyu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya kwarzanta gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Mohammed Idris ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta fi duk wata gwamnati da ta gabata a tarihin Najeriya a cikin shekaru biyu.

Source: Twitter
Mohammed Idris ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin taron farko na tattaunawar ƙasa kan shigar al’umma cikin al'amura da tsaro, wanda VON ta shirya a Abuja, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan
Bangarori 3 da yan adawa da kungiyoyi ke ganin gazawar gwamnatin Tinubu a shekaru 2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mohammed Idris ya yabawa Bola Tinubu
Ministan ya bayyana cewa suna da hujjojin da za su nuna irin nasarorin da gwamnatin Bola Tinubu ta samu.
“A makon jiya ne muka cika shekaru biyu da gwamnatin Tinubu, kuma muna da isassun hujjoji na irin gagarumar nasarar da gwamnatin ta samu."
“Babu wata gwamnati a baya da ta taɓa cimma abin da gwamnatin Tinubu ta cimma a cikin shekaru biyu."
"Na farko, jarumtar cire tallafin fetur da rushe tsarin damfara a kasuwar canjin kuɗi, gina manyan hanyoyi da tituna, tsarin ba ɗalibai lamuni da ba a taɓa yin irinsa ba, da kuma ƙirƙirar CreditCorp, dukkaninsu manufofi ne da ke dawo da kwarin gwiwa a zukatan matasanmu."
Ya ce duk da cewa gwamnatin ta fara da ƙalubale, amma yanzu an fara ganin amfanin manufofinta a faɗin ƙasar nan.
“Bayan samun ƙalubale a farko, farashin abinci na raguwa, mun rage barazanar rashin tsaro."
"A karon farko cikin shekaru da dama, tasirin mulki yana fara bayyana ta hanyoyi kamar, aiwatar da ƴancin kuɗin ƙananan hukumomi, ƙirƙirar ma’aikatun cigaban yankuna, da babbar nasarar da aka samu a fannin noma — wato ƙirƙirar ma’aikatar dabbobi ta tarayya."
Mohammed Idris

Source: UGC
Minista ya taɓo batun tsaro a mulkin Tinubu
Ministan ya kuma danganta ingantaccen mulki da tsaron ƙasa, yana mai cewa amincewa tsakanin gwamnati da al’umma ta fi ƙarfin yin amfani da makami.
“Babu tsaron ƙasa idan babu haɗin kan ƙasa. Kuma ba za a samu haɗin kai ba idan babu amincewa. A lokutan rashin tabbas da rashin tsaro, mafi karfin makami da muke da shi ba bindiga ba ce, amincewar da ke tsakanin talaka da masu mulki ce."
- Mohammed Idris
Sun cika surutu
Tukur Lawal ya shaidawa Legit Hausa cewa ministocin Shugaba Tinubu sun cika surutu don yabon shugaban ƙasa.
"Suna ta cewa an samu ci gaba, amma har yanzu talaka bai gani a ƙasa ba. Kuɗin da ake sayar da fetur raguwa suka yi ko ƙaruwa suka yi."
"Tsadar rayuwa da ake fama da ita ai ita ma tana daga cikin tarihin da gwamnatinsa ta kafa, domin abubuwa duk sun taɓarɓare."
- Tukur Lawal
An ba Shugaban kasa Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar PDP, Segun Showunmi, ya ba mai girma Bola Tinubu shawara kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.
Segun Showunmi ya nemi Shugaba Tinubu da ya tabbatar cewa ya tilastawa gwamnoni aiwatar da tsarin a jihohinsu.
Ya bayyana cewa idan ƙananan hukumomi suka samu ƴancin cin gashin kansu, za a samu ayyukan yi sosai a ƙasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

