Abba Kabir Ya Yi Hadaka da Tarayyar Turai domin Kawo Muhimman Ayyuka Kano

Abba Kabir Ya Yi Hadaka da Tarayyar Turai domin Kawo Muhimman Ayyuka Kano

  • Gwamnatin Kano ta bayyana aniyar zurfafa haɗin gwiwa da Tarayyar Turai (EU) a fannonin ilimi da makamashi
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi jakadan Tarayyar Turai, Gautier Mignot, a fadar gwamnatin jihar da ke Kano
  • Jakadan ya bayyana shirin EU na kara zuba jari a fannin ilimi, tattalin arzikin zamani da ci gaban matasa a jihar Kano

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce tana da cikakken shiri na zurfafa haɗin gwiwa da Tarayyar Turai (EU) domin bunkasa fannin ilimi da makamashi.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa tana shirye da yin hadin gwiwa game da sauran bangarori masu alaka da ci gaban dan Adam a jihar.

Abba Kabir
Abba Kabir Yusuf ya gana da wakilan Tarayyar Turai a Kano. Hoto: European Union Nigeria
Source: Facebook

Kungiyar tarayyar Turai ce ta bayyana wasu daga cikin abubuwan da ta tattauna da Abba Kabir a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Abba ya shiga madafin 'yan Kano a Saudiyya don duba abincin da ake rabawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi bakuncin jakadan Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS, Gautier Mignot, a fadar gwamnatin jihar da ke Kano.

Punch ta wallafa cewa Abba Kabir ya yaba da yadda EU ta zaɓi Kano domin gudanar da bikin Study in Europe Fair karo na farko a nahiyar Afrika.

Abba Kabir ya bukaci haɗin gwiwa da EU

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa ta samu ci gaba mai ma’ana a fannoni daban-daban tun bayan hawansa mulki.

A karkashin haka Abba Kabir ya bayyana bukatar karin tallafin EU wajen aiwatar da babban tsarin ci gaban jihar.

Abba ya ce sun yi imani da cewa idan suka kara zurfafa haɗin gwiwar, za su samu damar inganta fannin ilimi da kuma magance matsalar wutar lantarki domin bunkasa masana’antu da tattali.

Ya kara da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da maraba da duk wata cibiya ko kungiya wadda ke da niyyar taimakawa jihar wajen ciyar da al’umma gaba.

Kara karanta wannan

Bayan Abba Kabir, gwamna na 2 ya rufe makarantu saboda shagalin babbar Sallah

Abba Kabir
Gwamnan Kano ya bukaci karin hadin gwiwa da T. arayyar Turai. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Jakadan EU ya jinjina wa jihar Kano

A nasa bangaren, jakadan Tarayyar Turai, Gautier Mignot, ya bayyana cewa ziyarar da suka kai Kano na da nufin duba hanyoyin karfafa haɗin gwiwa da gwamnatin jihar.

Gautier Mignot ya ce za su yi hadin gwiwa da jihar musamman a bangaren ilimi, tattalin arzikin zamani da ci gaban matasa.

Ya ce tawagar sa za ta kai ziyara zuwa wasu ayyukan ci gaban tattalin arziki da aka kammala ko ake aiwatarwa a Kano da kudin EU, domin tantance cigaban da aka samu.

Jakadan ya kuma bayyana niyyar Tarayyar Turai na ƙara zuba jari a jihar Kano ta hanyar ayyuka masu ma’ana da za su shafi rayuwar al’ummar jihar, musamman matasa da ‘yan kasuwa.

Abba ya je madafin 'yan Kano a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara ta musamman wajen da ake dafa wa mahajjatan Kano abinci a Saudiyya.

Kara karanta wannan

Yaran talakawan Kano a makarantu 3, 000 za su amfana da kudin jarrabawa kyauta

Abba Kabir Yusuf ya samu rakiyar Sarkin Karaye da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar Kano yayin ziyarar ba-zatan da ya kai.

A bayanin da ya yi, gwamnan ya yaba da yadda ake dafa abinci mai tsafta ga mahajjatan, ya kuma yi kira da a cigaba da kokari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng