Ana Shirin Babbar Sallah, Gwamna Fintiri Ya Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashi
- Gwamna Ahmadu Fintiri ya fara biyan ₦70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan kananan hukumomi a jihar Adamawa
- Shugabannin NULGE sun yabawa Gwamna Fintiri bisa wannan mataki, inda suka ce yana nuna kishi da kulawa ga walwalar ma’aikata
- Fintiri ya ƙara sanar da sakin ₦5bn a Yunin 2025 domin biyan haƙƙin tsofaffin ma'aikata, wanda suka dade suna jira daga gwamnati
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Adamawa - Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da fara biyan mafi ƙarancin albashi na ₦70,000 ga ma’aikatan kananan hukumomin jihar.
Wannan mataki ya sanya jihar Adamawa cikin jerin jihohin farko da suka aiwatar da karin sabon mafi karancin albashi a Najeriya.

Source: Twitter
Ma'aikatan NULGE sun yabawa Gwamna Fintiri
Sanarwar ta fito ne bayan ziyarar ban girma da shugabannin kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi (NULGE) suka kai fadar gwamnatin jihar da ke Yola, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin kungiyar NULGE sun gode wa Gwamna Fintiri bisa jajircewarsa wajen tallafa wa ma’aikatan kananan hukumomi a fadin jihar.
Kungiyar NULGE ta yabawa Fintiri bisa yadda ya kafa tarihi wajen kyautata dangantakar gwamnati da ma’aikata, tare da nuna kishi wajen biyan su hakkokinsu.
Fintiri ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta rayuwar ma’aikata, yana mai cewa, “Ma’aikatanmu sun cancanci wannan da ƙari.”
Ya kuma bayyana cewa ya fara biyan sabon albashin ga ma'aikaran jihar tun watan Agusta 2024, sanan yanzu aka aiwatar da shi ga kananan hukumomi.
Fintiri zai biya hakkokin tsofaffin ma'aikata
A wani karin tallafi, Fintiri ya sanar da shirin sakin Naira biliyan 5 a watan Yunin 2025 don biyan haƙƙin tsofaffin ma'aikata da suka dade suna jira, inji rahoton The Guardian.
Yayin ziyarar ta NULGE, Fintiri ya ce:
“Wannan wani bangare ne na shirinmu na tallafa wa ma’aikata da kuma mutunta tsofaffin ma’aikatan da suka sadaukar da rayuwarsu wajen gina jihar.”
Wannan ya biyo bayan korafe-korafen da shugaban NLC na jihar, Emmanuel Fashe, ya gabatar, inda ya nemi daukin Fintiri kan walwalar ma’aikatan kananan hukumomi.
Matakin ya samu karɓuwa sosai daga ma’aikatan jihar, inda wasu irinsu Saliyatu Mohammad daga Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsare suka bayyana farin cikinsu.

Source: Twitter
An fara biyan albashin N70,000 a Adamawa
Fara biyan albashin ₦70,000 da kuma biyan kudin ritaya sun fito da manufofin gwamnatin Fintiri na bunƙasa tattalin arziki da nuna jin kai ga ma'aikata.
Rahoton ya tuno da shirye-shiryen da gwamnan ya aiwatar a kan hakan, misali Fintiri Business Wallet, wanda aka warewa Naira biliyan 3 domin tallafawa mata da matasa.
Wannan ya ƙara tabbatar da matsayin Fintiri a matsayin “gwamnan da ya fi kishin ma’aikata a Najeriya,” kamar yadda NULGE ta bayyana.
Fintiri zai bankado ma'aikatan bogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sha alwashin korar duk wani ma’aikacin da aka ɗauka aiki ba bisa ƙa’ida ba a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, gwamnan ya umarci ma’aikata da su gabatar da takardun shaidar ƙwararewarsu domin tantancewa.
Gwamna Fintiri ya kuma yi gargadi cewa duk wanda ya gaza mika takardar daukarsa aiki da ta kwarewa, ba zai karɓi albashin watanni masu zuwa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

