Gwandu: Rikicin Dawo da Sarki kan Mulki Ya Zo Ƙarshe, Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci

Gwandu: Rikicin Dawo da Sarki kan Mulki Ya Zo Ƙarshe, Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci

  • Kotun Kolin Najeriya ta dawo da zaman yanke hukunci kan rikicin sarautar Gwandu daga ranar 6 ga watan Yuni, zuwa 4 ga watan Yuni, 2025
  • Kotun ta ɗauki wannan matakin ne saboda hutun babbar Sallah da gwamnatin tarayya ta bayar wanda zai fara ranar Juma'a, 6 ga Yuni
  • Ana sa ran wannan hukunci da za a yanke shi ne zai zama raba gardama a rikicin masarautar Gwandu da ya shafe sama da shekaru 20

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Kotun Kolin Najeriya ta canza ranar da za ta yanke hukunci kan dambarwar sarautar Gwandu da ke jihar Kebbi a Arewa maso Yamma.

Rigimar sarautar dai ta shafi batun dawo da Alhaji Al-Mustapha Haruna-Jokolo a matsayin Sarkin Gwandu na 19.

Kotun koli.
Kotun koli ta matso da ranar yanke hukunci kan dambarwar sarautar Gwandu Hoto: Supreme Court
Source: Facebook

Yaushe kotun koli za ta yanke hukunci?

Kara karanta wannan

Bayan Abba Kabir, gwamna na 2 ya rufe makarantu saboda shagalin babbar Sallah

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kotun koli ta matso da ranar yanke hukunci daga 6 ga Yuni zuwa 4 ga Yuni, 2025.

Kotun ta sauya ranar hukuncin ne saboda hutun babbar sallah (Eid-el-Kabir) da gwamnatin tarayya ta sanar yau Litinin.

Kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Abba-Aji ne ya fara sauraron karar a ranar 11 ga Maris, inda dukkan bangarori suka gabatar da hujjojinsu, kafin a soma jiran hukuncin.

Karar dai na kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ke Sokoto da ta tabbatar da hukuncin da kotun jihar Kebbi ta yi a 2014.

Yadda ƙarar ta kai gaban kotun koli

Hukuncin kotunan baya ya bayar da umarnin a maido da Haruna-Jokolo kan kujerar sarautar da aka tsige shi daga kanta a shekarar 2005 cikin yanayi mai cike da ruɗani.

Duk da hukuncin kotun Kebbi ya amince da korafinta, gwamnatin jihar da Sarkin Gwandu na yanzu, Alhaji Muhammadu Ilyasu-Bashar, sun daukaka kara zuwa kotun ƙoli.

A cewarsu, karar ba ta dace da kotun jiha ba, don haka dukkan shari’ar da aka yi ba ta da inganci.

Kara karanta wannan

Bikin babbar Sallah: Gwamnatin tarayya ta ayyana hutun kwanaki 2

Abubuwan da kotun koli za ta yi hukunci kansu

A halin yanzu, kotun koli na nazari kan buƙatu guda hudu da kuma korafe-korafen martani guda biyu, kuma za ta yi hukunci guda daya da zai kunshi duka batutuwan da aka gabatar.

Lauyan da ke wakiltar Haruna-Jokolo shi ne Barista Sylvester Imhanobe, yayin da Yakubu Maikyau (SAN) ke kare gwamnatin jihar Kebbi, sai Hussaini Zakariya (SAN) wanda ke wakiltar Sarkin Gwandu na yanzu.

Gwamnan Kebbi.
Hukuncin kotun koli zai kaow karshen rikicin masarautar Gwandu Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Yayin da ranar yanke hukunci ke kara karatowa, jama’a a Birnin Kebbi na nuna damuwa da fatan cewa za a samu maslaha da zaman lafiya, ganin cewa rikicin ya jima yana tayar da jijiyoyin wuya a masarautar.

Wannan hukuncin dai ana sa ran zai zama raba gardama ga rikicin da ya shafe kusan shekaru 20.

Rikicin sarauta a Arewa

A ‘yan shekarun nan, rikice-rikice masu nasaba da sarauta sun fara karuwa a wasu yankunan Arewa, inda ake samun takaddama tsakanin ‘yan sarauta da kuma gwamnati ko majalisar masarauta.

Kara karanta wannan

An kama masu shirin tafiya Saudiyya da kwaya a lokacin aikin Hajji

A wasu lokutan, gwamnati na daukar matakin tsige sarki ko nada wani sabo, wanda ke janyo rikici mai tsanani da kuma kara rarraba kan al’umma.

A wasu masarautu, ana zargin siyasa da katsalandan din 'ya'yanta wajen nadin sarakuna, inda wasu ke ganin gwamnati na yin amfani da iko wajen hana mutanen gari zabin wanda suka fi so.

Wannan hali ya jefa al’ummomi da dama cikin rudani da rashin tabbas, musamman idan al’amura suka kai gaban kotu.

Abin da ya faru a Kano

A jihar Kano, rikicin sarauta ya dauki sabon salo bayan nadin sabbin sarakuna da sauke wasu, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin mabiya da masu ruwa da tsaki.

A Kebbi kuwa, rikicin sarautar Gwandu yana kai ruwa rana tsawon shekaru fiye da 20, inda ake zaman jiran hukuncin kotun koli wanda zai iya kawo karshen gardamar.

Wannan karuwa da rikice-rikicen sarauta a Arewa na nuna bukatar tsaftace tsarin nadin sarauta, da tabbatar da zaman lafiya da mutunta al’adun gargajiya ba tare da katsalandan na siyasa ba.

Gwamnatin Kebbi za ta tura ɗalibai Saudiyya

Kara karanta wannan

Yaran talakawan Kano a makarantu 3, 000 za su amfana da kudin jarrabawa kyauta

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Jihar Kebbi zs ta tura ɗalibai ƴan asalin jihar zuwa ƙasar Saudiyya domin karatun zamani da na addinin musulunci.

Gwamnatin karkashin jagorancin Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu ta sanar da cewa za ta ɗauki nauyin ɗalibai 70 su je Saudiyya su yi digiri na farko a fannoni daban-daban.

Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin addini, Imran bn Usman, kowace ƙaramar hukuma daga cikin 20 za ta ba da mutum 3, sai Birnin Kebbi na da gurabe 10.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262