2027: Shehu Sani Ya ba 'Yan Arewa Shawara kan Tazarcen Tinubu

2027: Shehu Sani Ya ba 'Yan Arewa Shawara kan Tazarcen Tinubu

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya buƙaci ƴan Arewa da su marawa Bola Tinubu baya a zaɓen 2027
  • Shehu Sani ya nuna cewa kamata ya yi yankin Arewa ya bari yankin Kudu ya kammala shekara takwas a mulki
  • Tsohon sanatan ya kuma caccaki tsofaffin shugabannin da suka fito daga Arewa kan yadda suka kasa kawo ci gaba a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki wasu tsofaffin shugabannin Arewa da suka taba riƙe madafun iko a matakin ƙasa.

Tsohon 'dan gwagwarmayar watau Shehu Sani ya zarge su da kasa sauya yankin Arewa zuwa cibiyar ci gaban tattalin arziƙi.

Shehu Sani, Bola Tinubu
Shehu Sani ya bukaci a zabi Tinubu a 2027 Hoto: @ShehuSani, @DOlusegun
Source: Facebook

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da ƴan jarida a gidansa da ke Kaduna a ranar Litinin, 2 ga watan Yunin 2025, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya yabi Shugaba Tinubu, ya fadi inda ya kerewa Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani ya ƙi bayyana sunayen waɗannan mutane, amma ya bayyana su a matsayin ƴan siyasa masu jin haushi saboda ba su cikin gwamnatin yanzu, kuma suna ƙoƙarin tunzura jama'a su yi wa gwamnati bore.

Shehu Sani ya buƙaci a goyi bayan Tinubu

Duk da wannan suka, tsohon sanatan ya yaba da ci gaban da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, tare da kiran al’ummar Arewa da su marawa shugaban ƙasan baya a zaɓen 2027, rahoton Vanguard ya tabbatar.

"Mu da muka fito daga yankin Arewa, muna godiya da irin ci gaban da wannan gwamnati ta kawo zuwa yanzu."
"Kuma ga waɗanda suka samu dama a baya su yi abin da ya fi haka amma suka kasa, muna gaya musu cewa ya fi dacewa su nemi afuwa bisa irin ɓarnar da suka yi wa mutanen Arewa."
“Kuma ga ƴan Arewa, ya kamata kada su bari a yaudare su ko a tunzura su kan gwamnatin da ke yin abin da ya fi na wadda ta fito daga yankinsu."

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta kare matakin Tinubu na runtumo basussuka

"Kada su bari a tunzura su kan shugaban ƙasan da ya marawa na mu baya na tsawon shekaru takwas a mulki. Na ji wasu kalamai da suka yi kama da ƙabilanci da son zuciya."

- Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya ba ƴan Arewa shawara

Shehu Sani ya bayyana cewa ya kamata yankin Arewa ya haƙura ya bari yankin Kudu ya kammala shekara takwas a kan mulki.

Shehu Sani
Shehu Sani ya caccaki tsofaffin shugabannin Arewa Hoto: Shehu Sani
Source: Twitter
“Amma mu duba wannan al’amari a cikin adalci, yankin Arewa maso Yamma ya fitar da shugabanni biyu tun daga 1999. Na farko shi ne Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, na biyu kuma shi ne Shugaba Muhammadu Buhari."
"Kuma a duk waɗannan zaɓuka, yankin Kudu maso Yamma ya mara wa Arewa baya, ba tare da wata babbar hamayya ba, musamman a lokacin mulkin Buhari."
“Don haka, abin da ya dace shi ne a bar Kudu su kammala shekara takwas a mulki, domin zaman lafiya, haɗin kai, da ɗorewar dimokuradiyyarmu."
"Ko da za a samu wani ɗan takara daga jam’iyyar adawa, ya kamata ya fito daga yankin Kudu maso Yamma domin wannan ne adalci, gaskiya da daidaito."
“Amma saƙo na zuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ne, ya kamata ya ƙara ɗaukar matakai wajen magance ƙalubalen da ke addabar yankin Arewa, ya saurari masu suka, sannan inda aka yi ƙarya a mayar da martani."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ayyana ranar hutu don jimamin 'yan wasan da suka rasu

- Shehu Sani

Shehu Sani ya faɗi kujerar da zai nema a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana ƙudirinsa na yin takara a zaɓen 2027.

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa zai nemi kujerar sanata a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Tsohon sanatan ya kuma bayyana cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin cewa Gwamna Uba Sani ya yi tazarce a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng