An Kama Masu Shirin Tafiya Saudiyya da Kwaya a Lokacin Aikin Hajji
- Hukumar NDLEA ta kama shugabannin wata ƙungiya da ke ɗaukar masu niyyar hajji zuwa kasar Saudiyya da kwayoyi a jihar Kano
- An cafke mutane uku: Abubakar Muhammad, Abdulhakeem Tijjani da Muhammad Aji Shugaba, bayan kama wasu fasinjoji biyu da hodar iblis
- An kuma kama wani ɗan kasuwa ɗan shekara 60 dauke da hodar iblis tare da kama miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 9.3
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama masu safarar kwayoyi da ke amfani da tafiya Hajji a matsayin hanyar kai kayan haram Saudiyya.
Bayan kama wasu masu niyyar zuwa aikin Hajji da hodar iblis a Kano, hukumar ta cafke shugabannin ƙungiyar uku da ke jagorantar safarar.

Kara karanta wannan
Hajjin bana: Za a fassara hudubar Arfah zuwa Hausa, Fulatanci da sauran harsuna 32

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka cafke mutanen ne a cikin wani sako da hukumar NDLEA ta wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta tabbatar da cewa mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 1 ga Yuni, 2025.
An kama masu safarar kwaya zuwa Saudiyya
A ranar 26 ga Mayu, NDLEA ta kama Ibrahim Mustapha da Muhammad Shifado a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano yayin da suke shirin hawa jirgi zuwa Jeddah.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sun boye hodar iblis inda aka fitar da su a cikin jirgi bayan dogon bincike.
Wannan ya jawo gudanar da bincike wanda ya bankado masu daukar nauyinsu, wato Abubakar Muhammad, Abdulhakeem Tijjani da Muhammad Aji Shugaba, wadanda aka kama a Kano.
Safarar kwaya: An kama wani ɗan kasuwa
A wani farmaki daban a Kano, NDLEA ta cafke wani ɗan kasuwa mai shekaru 60, Chinedu Leonard Okigbo, yayin da yake shirin tafiya Iran ta jirgin Qatar Airways.
An tabbatar da cewa an kama shi da hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.41, bayan dogon bincikensa da aka yi.
NDLEA ta bayyana cewa wannan na daga cikin manyan nasarorin hukumar a makon da ya gabata.
An gano tarin kwaya a jihar Rivers
A Port Harcourt, hukumar ta gudanar da bincike a akwatuna guda bakwai a tashar jirgin ruwa ta Onne tsakanin 28 zuwa 30 ga Mayu.
An gano kwalabe sama da dubu 825 na kwayoyi da wasu na'ukan kwayoyi sama miliyan 5 da darajarsu ta kai Naira biliyan 9.35.
Haka zalika, a hanyar Kano–Maiduguri, hukumar NDLEA ta kama wasu masu hada kudin ganye dauke da $900,000 na bogi.

Source: Twitter
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba da kwazon jami'ansa a jihohin Kano, Kwara da Adamawa da sauransu.
An kama wadanda suka kashe DPO a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano na cigaba da samame kan kisan DPO da aka yi a karamar hukumar Rano.
Rahotanni sun nuna cewa an kama wani da ake zargi shi ya tunzura matasa tare da jagorantarsu wajen aikata laifin.
Kakakin 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewa an kama mutane sama da 40 da ake zargi suna da alaka da kisan.
Asali: Legit.ng

