Fadar Shugaban Kasa Ta Kare Matakin Tinubu na Runtumo Basussuka
- Fadar shugaban ƙasa ta yi ƙarin haske kan basussukan da gwamnatin mai girma Bola Tinubu take karɓowa
- Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa karɓo basussuka ba laifi ba ne idan har an yi abin da ya dace da su
- Ya nuna cewa ko ƙasashen da suka ci gaba a dunuya suna karɓo basussuka don su gudanar da wasu ayyukan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta kare matakin da gwamnatin Bola Tinubu take ɗauka na ciyo basussuka.
Fadar shugaban ƙasan ta ce tsarin karɓar bashi da gwamnati ke yi, hanya ce ta dole don ci gaban tattalin arziƙi, tare da jaddada cewa yin hakan ba laifi ba ne idan an yi amfani da shi yadda ya dace.

Source: Facebook
Wannan bayani ya fito ne yayin wata ganawa da ƴan jarida da aka gudanar a Legas, inda manyan hadiman shugaban kasa suka yi bayani ga manema labarai, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Hadiman shugaban ƙasan sun yi bayanai kan yadda gwamnatin ke tafiyar da tattalin arziƙi da kuma irin hangen nesan da take da shi nan gaba.
A makon da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu ya aike da bukata zuwa majalisar tarayya domin neman amincewa da ƙarin bashin waje da na cikin gida da jimlarsu ta kai Naira tiriliyan 34.15.
An kare Bola Tinubu kan ciyo basussuka
Sai dai, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, yayin da yake amsa tambayoyi dangane da yawan bashin da Najeriya ke karɓowa, ya kare matakin.
"Karɓar bashi ba laifi ba ne. Ko ƙasashen da suka ci gaba irin su Amurka da Birtaniya suna karɓar bashi fiye da abin da GDP ɗinsu ya kai."
"Matsalar ba karbar bashi ba ce, matsalar ita ce yadda ake amfani da kuɗin da aka karɓo."
"Ƙasar mu matalauciya ce mai yawan jama'a. Dole ne mu daina yaudarar kanmu, kasafin kudin Najeriya bai kai na Afirika ta Kudu ba. Dole mu fuskanci gaskiya game da abin da za mu iya ɗauka ba tare da karbar bashi ba."
Gwamnatin Tinubu ta gyara tattalin arziƙi
Ya ƙara da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta samu nasarori da dama a ɓangaren gyaran tattalin arziki da shirye-shiryen da suka shafi kowa, duk da ƙalubalen da aka gada daga tsohuwar gwamnati.

Source: Facebook
Yayin da yake bayani kan nasarorin tattalin arziƙi duk da wahalhalun farko, Onanuga ya ce: .
"Mun amince cewa shekarar farko ta wannan gwamnati ta kasance mai cike da ƙalubale. Mun fuskanci manyan matsaloli, ciki har da hauhawar farashi, rashin daidaito a kuɗin waje, da kuma matsalolin da ba su cikin ikonmu kai tsaye."
“A yau, alamu na tattalin arziki sun fara kyautatuwa sosai. Wannan a bayyane yake. Cibiyoyin duniya kamar bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) sun yaba da ƙoƙarinmu da hanyar da muke bi."
"Fiye da dalibai 600,000 sun amfana da tsarin ba da lamunin karatu ƙarƙashin NELFUND, da sauran shirye-shirye."
Shugaba Tinubu ya roƙi ƴan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi alfarma a wajen ƴan Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙsra haƙuri kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa a ƙasar nan.
Bola Tinubu ya bayyana cewa idan aka kai zuciya nesa, za a ga amfanin abubuwan da yake a ƙasar nan a nan gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


