INSO: Najeriya Ta Dakatar da Kungiyar Ketare kan Zargin Alaka da Boko Haram

INSO: Najeriya Ta Dakatar da Kungiyar Ketare kan Zargin Alaka da Boko Haram

  • Rahoto ya ce gwamnatin tarayya ta dakatar da kungiyar INSO mai bada tallafin jin kai da ke aiki a Najeriya tun daga shekarar 2016
  • An danganta dakatarwar da zarge-zargen alaka da Boko Haram, lamarin da ke haifar da fargaba kan matsin lamba ga kungiyoyin agaji
  • INSO ta bayyana shirinta na tattaunawa da gwamnati, sai dai masu lura da al’amura na fargabar hakan na iya barazana ga mabukata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan kungiyar INSO mai zaman kanta da ke taimaka wa kungiyoyin agaji a wuraren da ke fama da rikici.

Wannan hukunci na zuwa ne bayan zarge-zargen ayyukan kungiyar da gwamnati ke ganin suna da alamun ban shakku.

Tinubu
Najeriya ta dakatar da INSO kan zargin alaka da Boko Haram. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wani rahoto da DW Africa ta wallafa a shafinta na Facebook ya nuna cewa an dauki matakin ne kan zargin alakar kungiyar da Boko Haram.

Kara karanta wannan

Karatu kyauta: Gwamnatin Tinubu za ta fara ba 'yan makarantun fasaha kudi a wata

INSO, wacce ke da hedikwata a birnin Hague na Netherlands, ta dade tana tallafawa sama da kungiyoyi 1,000 a kasashen da ake rikici, ciki har da Najeriya tun daga shekarar 2016.

Dakatarwar na zuwa ne watanni bayan wani ɗan majalisar wakilai na Amurka, Scott Perry, ya zargi USAID da tallafawa Boko Haram da wasu kungiyoyin ta’addanci.

Sai dai tun a wancan lokacin VOA ta fitar da rahoto cewa gwamnatin Amurka ta musanta zargin gaba daya.

Zargin da ake yi kan INSO kan Boko Haram

Wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Najeriya na kyautata zaton INSO na da hannu a wasu ayyukan rashin gaskiya, musamman dangane da tsaro.

Wannan ya jefa INSO cikin jerin kungiyoyin da ake duba da idanun tuhuma tare da daukar matakin dakatar da ita.

Ana ganin hakan na iya zama mataki na farko na shigar da dokoki masu tsauri kan ayyukan kungiyoyin agaji a Najeriya bayan maganar da dan majalisar Amurka ya yi.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun nuna damuwa bayan ambaliya ta ruguza gidaje da mutane a Neja

Ayyukan da kungiyar INSO ke yi a duniya

INSO ta bayyana cewa an kafa ta ne domin tallafa wa kungiyoyin agaji da ke aiki a wuraren da rikici ke gudana bayan kwarewa da ta samu a Afghanistan.

A wani sako da ta wallafa a shafinta, INSO ta ce aikin da take ya zama ginshiki wajen bada tsaro da shawarwari ga kungiyoyin da ke bayar da agaji.

Ta kara da cewa tana aiki tare da ofishin UNOCHA da sauran kungiyoyin agaji na gida da na waje wajen tabbatar da daidaito da hadin gwiwa a fannin agaji.

Fargabar mummunan tasirin dakatar da INSO

Masu lura da al’amura sun nuna damuwa cewa dakatar da INSO na iya shafar ayyukan tallafi da kungiyoyi ke gudanarwa ga miliyoyin ‘yan Najeriya da ke fuskantar rikici, yunwa, da talauci.

INSO na daga cikin manyan ginshikan da ke bada goyon baya wajen tsare-tsare da kariya ga ma’aikatan agaji.

Ribadu
INSO ta nemi tattaunawa da Najeriya bayan dakatarwa. Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Twitter

Sai dai rahoton Sahara Reporters ya nuna cewa kungiyar ta ce tana shirye ta yi aiki da hukumomin Najeriya wajen warware duk wata matsala cikin lumana.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama wanda ya jagoranci kashe DPO a Kano da wasu mutane 40

Sojojin Najeriya sun kashe Boko Haram 60

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 60 a jihar Borno.

Rahoto ya nuna cewa sojojin sama ne suka yi ruwan boma bomai kan 'yan ta'addan yayin wani farmaki da aka kai kansu.

Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa sojojin kasan Najeriya sun kara murkushe 'yan ta'addan bayan ruwan bom da aka musu ta sama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng