'Yan Ta'adda Sun Dasa Bam a Borno, an Hallaka Bayin Allah

'Yan Ta'adda Sun Dasa Bam a Borno, an Hallaka Bayin Allah

  • Rayukan bayin Allah sun salwanta bayan wani abin fashewa ya tashi a wata tashar mota da ke jihar Borno
  • Tashin abin fashewar ya yi sanadiyyar rasa rayukan aƙalla fasinjoji tara yayin da suke jiran motoci su shiga
  • Shugaban majalisar dokokin jihar Borno ya tabbatar da aukuwar lamariin mara daɗi, inda ya buƙaci sojoji su ƙara ƙaimi wajen korar ƴan ta'adda

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - An shiga jimami bayan wani abin fashewa da aka ɓoye a tashar mota ya hallaka fasinjoji a jihar Borno.

Aƙalla mutane tara sun rasa rayukansu bayan wani abin fashewa ya tashi a tashar motoci da ke ƙauyen Mairari, ƙaramar hukumar Guzamala ta jihar Borno.

Bam ya tashi a Borno
'Bam ya kashe mutane 9 a Borno Hoto: @ProfZulum
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar Asabar, inda mutane da dama suka jikkata a wurin da lamarin ya auku.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ayyana ranar hutu don jimamin 'yan wasan da suka rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin fashewa ya hallaka mutane a Borno

Shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Rt. Hon. Abdulkarim Lawan, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa mutanen da aka kashe fasinjoji ne da ke jira su shiga mota a tashar motar da ke ƙauyen.

"Abin takaici ne cewa jajirtattun mutane tara daga cikin mazabata sun rasa rayukansu sakamakon fashewar bama-bamai da aka dasa a ƙasa yayin da suke jiran tashin motoci a tashar ƙauyen Mairari.”
“Allah Ya sanya su a Aljannatul Firdaus. Ina kuma addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga waɗanda aka kai asibitoci a Monguno da Maiduguri domin samun kulawar likitoci."
“Kamar yadda kuka sani, ƙauyen Mairari ne wanda a baya aka sake maido da mutane sau biyu tare da kafa ikon farar hula a cikin dukkanin ƙaramar hukumar Guzamala."
"Sai dai yanzu an sake barin ƙauyen saboda hare-haren Boko Haram/ISWAP.”
“Mutane da dama daga Monguno, Guzamala, da Maiduguri suna ziyartar Mairari don yin noma, saboda suna da kishin ƙasa da jajircewa.”

Kara karanta wannan

Ambaliya: Sheikh Pantami ya yi magana kan mutuwar mutane sama da 100 a Jihar Neja

“Abin takaici, ƴan ta’adda da suke bibiyar motsin su ne suka dasa bam a tashar mota, wanda ya tashi lokacin da mutane ke jiran motar haya don komawa inda suka fito."

- Abdulkarim Lawal

An kashe mutane a Borno
Abin fashewa ya tashi a Borno Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ɗan majalisa ya yi ta'aziyya

Ɗan majalisar ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka samu raunuka daban-daban.

Abdulkarim Lawan ya roƙi sojoji da sauran hukumomin tsaro da su dawo da zaman lafiya a Guzamala, musamman a Gudumbali, hedkwatar ƙaramar hukumar da kuma ƙauyen Mairari da yankunan da ke kewaye, waɗanda suka daɗe suna ƙarƙashin ikon Boko Haram ba tare da gwamnati ba.

Sojoji sun kashe babban kwamandan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wani babban kwamandan ƴan ta'addan Boko Haram.

Sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun hallaka Amir Abu Fatima ne bayan sun kai wani farmaki a maɓoyarsa da ke jihar Borno.

Jami'an tsaron sun kuma hallaka wasu da yawa daga cikin mayaƙansa tare da ƙwato makamai masu tarin yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng