"Kai Tsaye Na Gaya Masa": Amaechi Ya Fadi Abin da Ya Gayawa Tinubu kan Zaben 2023
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi magana kan abubuwan da suka faru kafin babban zaɓen 2023 tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu
- Amaechi ya bayyana cewa ya sanar da shugaban ƙasan ba zai goya masa baya ba don ya lashe zaɓe a 2023
- Tsohon gwamnan ya nuna cewa ya yi hakan ne saboda ya yi amanna cewa Tinubu bai da ƙwarewar da zai jagoranci Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa tun farkon kamfen ɗin da ya kai ga zaɓen 2023, ya sanar da Shugaba Bola Tinubu cewa ba zai taɓa mara masa baya ko kaɗa masa ƙuri’a ba.
Rotimi Amaechi ya ce ya tsaya akan wannan matsaya ne saboda ya yi imani cewa Tinubu ba shi da ƙwarewar da ake buƙata don tafiyar da Najeriya.

Kara karanta wannan
Kudin mazaɓa: Tinubu ya ba kowane ɗan Majalisar Tarayya Naira biliyan 1? Bayanai sun fito

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne a wani taron da aka gudanar a Abuja ranar Asabar domin bikin cikarsa shekara 60 a duniya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Amaechi ya gayawa Tinubu a 2023?
Tsohon gwamnan na jihar Rivers, ya bayyana cewa bai yi ɓoye-ɓoye ba wajen sanar da Tinubu cewa ba zai goya masa baya ba.
“Na gayawa Tinubu a Yola cewa ‘Ba zan goyi bayanka ba, ba zan yi aiki da kai ba.’ Ban yi aiki da shi ba, ban kaɗa masa ƙuri’a ba. Batun ƙwarewa ne kawai."
“Ina fadar haka ne saboda wasu mutane a jihar Rivers na cewa ‘bai yi wa APC aiki ba, bai marawa Tinubu baya ba’. Na sanar da shi kafin zaɓe domin na yi imani akwai matsala ta rashin ƙwarewa."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya ce ɗora talakawa kan keken ɓera
Amaechi ya koka da cewa an yi amfani talakawa wajen sanya su yin zaɓe bisa ƙabilanci da addini, wanda hakan ya sanya aka tsinci Najeriya cikin halin da take ciki a yanzu.
"Wasu daga cikinmu da ke nan muna zaɓe bisa ƙabilanci ko addini. Talakawa da waɗanda ba su da ilmi ana amfani da su wajen kaɗa ƙuri’a bisa ƙabilanci da addini, shi ya sa muke cikin wannan hali."
“Idan mun tashi daga nan, sai mu shiga shiri domin ƙwace mulki, babu wani shugaba a Najeriya da ya damu da ku."
- Rotimi Amaechi

Source: Twitter
Amaechi ya taɓo batun haɗaka
Game da batun haɗakar ƴan adawa, Amaechi ya ce:
“Muna so mu miƙa wuya ga ɓangaren adawa, idan za su iya fitar da mu daga wannan matsala.”
“Idan muna son sauya gwamnati, idan muna son kawar da wanda ke kan karagar mulki, za mu iya. Amma dole ne mu fara da fifita buƙatun ƙasa fiye da na kanmu kafin mu cimma hakan.”
"Gwamnatin yanzu tana amfani da talauci a matsayin makami ta hanyar sace kuɗaɗen da ya kamata a gina asibiti da makarantu da su. Fa’idar cire tallafin fetur tana cikin aljihunsu."
Tinubu ya taya Amaechi murna
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da saƙon taya murna ga tsohon ministaɓ sufuri, Rotimi Amaechi.
Shugaba Tinubu ya ainka da saƙon ne domin taya Amaechi murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare da cika shekara 60 a duniya.
Mai girma Bola Tinubu ya yabawa tsohon gwamnan na jihar Rivers, kan irin hidimar da ya yi wa Najeriya.
Asali: Legit.ng

