Sanusi II Ya Bayyana Lokacin da Ya San Talauci a Rayuwarsa
- Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan matsalar talaucin da ake fama da ita a Najeriya
- Sanusi II ya bayyana mafi yawan manyan mutane da shugabanni ba su san ainihin menene talauci ba
- Ya yi kiran da a tashi tsaye a haɗa kai don magance matsalar talauci da ta hana bayin Allah a ƙasar nan yin rayuwa mai inganci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sarkin Kano na 16 kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan talaucin da ake fama da shi a Najeriya.
Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ya fahimci ma’anar talauci ne kawai bayan ya hau karagar mulki a matsayin sarki.

Source: Facebook
Sanusi II ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen wani taro da aka gudanar don bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi na shekara 60, a birnin Abuja, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
Ambaliya: Sheikh Pantami ya yi magana kan mutuwar mutane sama da 100 a Jihar Neja
Sanusi II ya ce manyan mutane ba su san talauci ba
Sarkin na Kano na 16 ya bayyana cewa manya da yawa a ƙasar nan ba su san menene talauci ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
“Yawancin manyan mutane a Najeriya ba su san ma’anar talauci ba. A matsayina na masanin tattalin arziƙi kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, alƙaluma kawai na ke gani. Amma ban san talauci ba sai da na zama sarki."
“Idan ka tafi ƙauyuka ka ga irin ruwan da mutane ke sha, gidajen da suke ciki, azuzuwan karatu guda biyu marasa rufi."
“Shin muna ƙaunar mutane ne ko kuwa kawai muna ƙaunar mulkar su? Menene fifikonmu? Muna gina gadar sama da ƙasa a birane domin kanmu, alhali mutanen karkara ba za su iya isa asibiti ba."
"Muna cikin mawuyacin hali, abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne yadda za mu fita daga wannan matsala."

Kara karanta wannan
Musulmi sun yi babban rashi, Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya yi kira ga shugabanni da su kasance masu jin ƙai da nuna tausayi ga mutanen da aka damƙa musu jagoranci.

Source: Facebook
El-Rufai ya ce ana kuskure wajen yin zaɓe
A nasa jawabin, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna damuwa kan yadda ƴan Najeriya ke maimaita kuskure ta hanyar zaɓar baragurbin shugabanni.
“Muna ci gaba da zaɓar mutane da ba su da wata kwarewa face su ƙarbi mulki kawai, amma ba su san yadda za su gudanar da mulki ba."
- Nasir El-Rufai
Malami ya gargaɗi Sanusi II
A wani labarin kuma, kun ji cewa malamin addinin Kirista kuma shugaban cocin Evangelical Spiritual International, Primate Elijah Ayodele, ya ja kunnen Muhammadu Sanusi II.
Prinate Ayodele ya gargaɗi sarkin Kano na 16 kan ya bi sannu a hankali kuma ya yi taka tsan-tsan kan yadda yake gudanar da rayuwarsa.
Babban malamin addinin na Kirista ya ja kunnen Muhammasu Sanusi II kan ya sanya ido sosai kan irin abin da yake zuwa cikin cikinsa musamman abin da yake sha.
Asali: Legit.ng