Mutuwa Ta Kara Taɓa Sarakunan Najeriya, Sarki na 2 Ya Rasu cikin Awanni 24
- Sarkin ƙasar Iroko a jihar Oyo, Sunmaila Olasunkanmi Abioye Opeola ya riga mu gidan gaskiya da safiyar ranar Juma'a
- Prince Dolapo Abioye ne ya tabbatar da rasuwar basaraken a wata sanarwa da ya fitar, ya ce za a yi jana'iza yau Asabar bisa koyarwar addinin musulunci
- Marigayin ya kasance mutum mai ƙoƙarin kwatanta gaskiya, adalci, da tausayi, wanda ya bai wa kowa dama, ba tare da nuna bambanci ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Oniroko na Irokoland da ke ƙaramar hukumar Akinyele a jihar Oyo, Mai Martaba Sunmaila Olasunkanmi Abioye Opeola (Kurunloju 1) ya rasu.
Al’umma da iyalan masarautar Irokoland da ke karamar hukumar Akinyele sun shiga cikin jimami da alhini, bayan rasuwar Mai Martaba Sarki Sunmaila.

Source: UGC
Jaridar The Nation ta tattaro cewa marigayin ya rasu da safiyar ranar Juma’a, 30 ga Mayu, 2025, bayan shafe tsawom shekaru a kan mulki.

Kara karanta wannan
Musulmi sun yi babban rashi, Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masarautar Iroko ta sanar da jana'izar sarki
Sanarwar rasuwar ta fito ne daga Prince Dolapo Abioye a madadin dangin Opeola-Oniroko.
Ya bayyana cewa za a gudanar da jana’izar marigayin a yau Asabar da karfe 10:00 na safe, kamar yadda shari'ar addinin Musulunci ta tanada.
Haka kuma, ya ce za a fitar da karin bayani dangane da sauran shirye-shiryen jana’izar da abubuwan da za su biyo baya nan gaba.
Al'umma sun yi rashin Sarki a Oyo
Sanarwar ta ce:
"Cike da alhini da girmamawa, nake sanar da rasuwar Mai Martaba Sarkinmu, Oba Sunmaila Olasunkanmi Abioye Opeola (Kurunloju I), Oniroko na Iroko, wanda ya koma ga mahaliccinsa da safiyar Juma’a, 30 ga Mayu, 2025.
"A lokacin mulkinsa, Mai Martaba ya kasance ginshiki na hadin kai, al’ada da ci gaba. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima, kare al’adunmu, da kuma tabbatar da ci gaba a Iroko, Karamar Hukumar Akinyele da Jihar Oyo gaba ɗaya.”

Kara karanta wannan
Babbar Sallah: Za a raba dubban shanun layya kyauta ga Musulmi a Kano, Abuja da jihohi 10
Takaitaccen bayani kan Sarkin Iroko
Marigayi Oba Sunmaila Opeola ya kasance jagora mai kishin ci gaban al’ummar da yake jagoranta.
A tsawon lokacin mulkinsa, ya yi fice wajen hada kan jama’a, kare al’adu na gargajiya, da kuma himma wajen inganta rayuwar al’ummar ƙasar Iroko.
Basaraken ya kasance mutum mai ƙoƙarin kwatanta gaskiya, adalci, da tausayi, wanda ya bai wa kowa dama, ba tare da nuna bambanci ba.

Source: Facebook
A karkashin jagorancinsa, an samu ci gaba a fannoni da dama ciki har da ilimi, lafiya, da zaman lafiya a tsakanin kabilu da addinai.
Oba Sunmaila Opeola ya yi amfani da kusancinsa da gwamnatin jihar Oyo wajen jawo hankalin masu ruwa da tsaki don kawo ayyukan ci gaba ga Iroko da kewaye.
Sarkin Epe a jihar Legas ya kwanta dama
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Epe da ke jihar Legaas, Mai Martaba Shefiu Ọlatunji Adewale ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 86 a duniya.
Marigayi Sarkin, wanda ya hau karagar mulki a shekarar 2009, tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya shafe tsawon shekaru 37 a bakin aiki kafin ya yi ritaya.
Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga fadar basaraken, bayanai sun nuna cewa za a yi jana'izar sarkin yau Asabar.
Asali: Legit.ng
