Karatu Kyauta: Gwamnatin Tinubu za Ta Fara ba 'Yan Makarantun Fasaha Kudi a Wata
- Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin karatu kyauta, samar da abinci da alawus na N22,500 a kowane wata ga ɗaliban makarantun fasaha
- Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a taron ƙaddamar da shirin horar da matasa kan sana’o’i (TVET) a Abuja
- An tsara shirin ne domin jawo hankalin matasa da rage zaman banza ta hanyar koya musu fasahohin da za su amfanar da kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da wani muhimmin sauyi a tsarin ilimi da ya shafi koyar da sana’o’i da fasaha.
Gwamnatin Bola Tinubu ta ce za a daina karɓar kuɗin makaranta daga ɗaliban da ke karatu a makarantun fasaha.

Source: Twitter
Rahoton Arise News ya nuna cewa ministan ilimi, Dr Tunji Alausa, ne ya fadi haka yayin ƙaddamar da sabon shirin horar da matasa a fannin fasaha (TVET) a Abuja a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa wannan tsari ya haɗa da cire kudin makaranta, samar dakin kwana da abinci, da kuma alawus na Naira 22,500 duk wata ga kowanne ɗalibi.
Dalilin fara karatu kyauta da tallafawa dalibai
Ministan ya ce an bullo da shirin ne domin jawo hankalin matasa su rungumi ilimin fasaha da sana’a, ta yadda za su samu ƙwarewa da za ta amfani kansu da ƙasar gaba ɗaya.
Ya ce shirin ya dace da burin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da cewa babu wani ɗan Najeriya da aka bari a baya, musamman wajen samar da kayan aiki da ilimi ga matasa.
Tribune ta wallafa cewa Dr Alausa ya ce:
“Muna son wannan shiri ya zama wata hanya ta gyara tsarin iliminmu domin ya dace da bukatun tattalin arzikin ƙasa da burin matasanmu.”
Za a horar da matasa miliyan 5 nan da 2030
Ministan ya bayyana cewa gwamnati na da niyyar horar da akalla matasa miliyan 5 harkar masana’antu nan da 2030, tare da samar da kayan fara sana’a da rance mai sauƙin biya.
Alausa ya ce:
“Manufarmu ba wai kawai mu samar da masu takardar shaidar ƙwarewa ba ce, muna so mu gina sahihan masu fasaha da za su iya gogayya da takwarorinsu a duniya.”
Ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da tantance cibiyoyin horarwa na gwamnati da na masu zaman kansu a fadin ƙasa domin su iya karɓar dalibai da ke son shiga shirin.

Source: Twitter
Yadda shirin zai rage zaman banza a Najeriya
Ministan ya jaddada cewa wannan shiri zai taimaka wajen rage zaman banza tsakanin matasa, ƙarfafa masana’antu, da kuma jawo zuba jari daga ketare saboda samun sahihan masu fasaha.
Shirin TVET zai kasance karkashin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnoni, hukumomi masu kula da ilimi da kamfanoni.
Za a fara hukunta barayin amsa a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta karbi shawarwari daga kwamitin inganta jarrabawa na kasa.
Daga cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar akwai kafa kotu ta musamman domin gurfanar da barayin amsa.
Ministan ilimi, Dr Tunji Alausa ya bayyana wa kwamitin cewa za su yi kokarin ganin sun tattabar da dukkan abubuwan da kwamitin ya fada.
Asali: Legit.ng

