Kano: APC ba Ta Hakura ba, Tana Tunanin Daukaka Kara kan Zaben Kananan Hukumomi
- Jam’iyyar APC a Kano ta ce za ta tattauna da lauyoyinta kafin ta yanke shawara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben jihar
- A ranar Juma'a, 30 ga watan Mayu, 2025 ne kotun daukaka kara ta bayyana cewa kotun tarayya ba ta da hurumin hana zaben kananan hukumomin Kano
- A martanin APC, Sakataren yada labaranta, Ahmed S Aruwa ya ce suna sa ran samun nasara matukar suka daukaka kara zuwa kotun koli
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Jam’iyyar APC a jihar Kano ta bayyana rashin gamsuwa da hukuncin kotun daukaka kara da ya halasta zaben kananan hukumomi a Kano.
Jam'iyyar ta kuma bayyana cewa ba lallai ta nade hannayenta a kan hukuncin ba, domin har yanzu kokenta na rashin ingancin zaben yana nan daram.

Source: Facebook
A wata hira da Premier rediyo da aka wallafa a Facebook, sakataren yada labarai na APC a Kano, Ahmed S. Aruwa, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta nazarci hukuncin sosai.
Kano: APC na iya zuwa kotun koli
Daily Post ta ruwaito cewa Ahmed S. Aruwa ya ce hukuncin bai karya musu gwiwa ba, yana mai tuna irin wannan lamari da ya taba faruwa a jihar Ribas.
Ya bayyana cewa APC za ta duba yiwuwar daukaka kara zuwa kotun koli bayan ta kammala tattaunawa da lauyoyinta kan hukuncin kotun daukaka kara da aka yanke a ranar Juma’a.
A ranar Juma'a ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke, wanda ya hana Hukumar Zabe ta Kano (KANSIEC) gudanar da zaben kananan hukumomi..
Amma Aruwa ya ce wannan hukuncin bai nufin jam’iyyar ba za ta samu nasara a gaba ba, musamman idan ta daukaka karar zuwa kotun koli.

Kara karanta wannan
Ambaliya: Ana tsoron rayuka sama da 50 sun salwanta bayan gano gawarwaki 15 a Neja

Source: Facebook
Ahmed S. Aruwa ya ce:
“Wannan shari’a da aka yi, ina da yakini cewa jam’iyyar APC za ta zauna ta duba hukuncin da kyau, sannan ta fitar da matsayinta—wanda ka iya zama zuwa kotun koli.”
'APC za ta iya yin nasara a kotu' — Aruwa
Sakataren yada labaran APC na Kano, Ahmed S Aruwa ya bayyana cewa akwai alama mai karfi na cewa jam'iyyar za ta iya samun nasara idan ta daukaka kara zuwa kotun koli.
Ya ce an taba samun irin wannan shari’a a jihar Ribas, inda kotun koli ta tabbatar da cewa babbar kotun tarayya na da hurumi kan shari’ar zaben kananan hukumomi.
Aruwa ya ce:
“An taba samun irin wannan a Ribas, inda kotun daukaka kara ta ce kotun tarayya ba ta da hurumi, amma kotun koli daga baya ta tabbatar cewa kotun tarayyar na da hurumin sauraron irin wannan kara.”
Ya kara da cewa daga bisani kotun koli ta kori shugabannin kananan hukumomin jihar Ribas, yana mai fatan hakan zai iya faruwa a shari’ar Kano idan aka daukaka kara.
Kotu ta yi hukunci kan zaben Ciyamomin Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi hukunci kan zaben ƙananan hukumomi a jihar Kano, inda ta soke hukuncin da wata babbar kotun tarayya.
Mai Shari’a Biobele Georgewill tare da wasu alkalan biyu, sun ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙorafin da ya shafi tsarin hukumar zabe ta jihar Kano (KASIEC).
Kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana cewa babbar kotun jiha ce kadai ke da hurumi akan irin wannan shari’a, don haka ta tabbatar da inganci da sahihancin zaben ciyamomin 44 na Kano.
Asali: Legit.ng

