Gwamna Ya Cika Baki kan Yiwuwar Fadawa Komar EFCC bayan Barin Mulki
- Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya taɓo batun yiwuwar ya samu kansa a hannun hukumar EFCC bayan ya bar mulki
- Umo Eno ya bayyana cewa ba zai yi abin da zai sanya a riƙa ganinsa wajen EFCC bayan ya sauka daga mulkin jihar
- Gwamnan ya bayyana cewa tsofaffin gwamnoni na shiga matsala ne bayan barin mulki saboda sun bari mutane sun sanya su karkatar da dukiyar gwamnati
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya yi magana kan batun yiwuwar hukumar EFCC ta bincike shi bayan ya bar ofis.
Gwamna Umo Eno ya sha alwashin cewa ba za a riƙa ganinsa yana yawan zuwa ofishin hukumar EFCC ba bayan ya sauka daga kan kujerar mulki.

Source: Twitter
Gwamna Umo Eno ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ƴan jarida da aka shirya domin bikin cikarsa shekaru biyu a kan mulki a ranar Alhamis, 29 ga watan Mayu 2025, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan
"Lokaci ya yi da zan bar PDP," Gwamna ya ƙara nuna alamun zai koma APC kafin 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Eno ya faɗi kuskuren tsofaffin gwamnoni
Fasto Umo Eno ya danganta matsalar da yawancin tsofaffin gwamnoni ke shiga bayan mulki da matsin lambar da jama'a ke yi musu don su karkatar da dukiyar gwamnati.
Gwamnan ya bayyana cewa ya dage wajen gudanar da mulki cikin gaskiya, riƙon amana, da kuma amfani da kuɗi yadda ya dace, duk da buƙatu da matsin lamba daga ƙungiyoyin magoya bayansa daban-daban.
"Lokacin da na zama gwamna, na shaida wa mutanen Akwa Ibom cewa za mu kafa asusun ajiya na gaggawa. Duk wata muna tabbatar da cewa ba mu kashe duk kuɗaɗen shigar mu gaba daya ba."
“Ni ba na cikin masu yawan kashe kuɗi a banza, ƴaƴana za su iya tabbatar da hakan. Dole ne ya zama na cewa kuɗi akwai amfanin da za su yi."
- Fasto Umo Eno
Eno ya ce ba zai tsinci kansa a hannun EFCC ba
Gwamnan ya bayyana cewa buƙatun jama’a na ƙara yawa sakamakon jin cewa gwamnati dole ne ta biya kowace buƙata, ko da kuwa hakan na da illa ga kuɗinta.

Kara karanta wannan
'Cigaban mai haka rijiya,' Buba Galadima ya ce babu abin a yaba a shekaru 2 na Tinubu

Source: Facebook
"Na ga yadda wasu matasa ke cewa su ƴan ƙungiyoyin goyon baya ne na Umo Eno, kuma tun da suka gama goyon bayana, bai yi musu komai ba. Saboda haka za su je su yi zanga-zanga. Na yi dariya. Ina roƙon kada Allah Ya su shiga matsala da jami'an tsaro."
“Suna cewa sun goyi bayana don samun nagartaccen mulki, kuma ina ƙoƙarina wajen samar da hakan, amma su na son na basu kuɗi. Ina zan samo kuɗin da zan ba su?"
“Idan ka ga tsofaffin gwamnoni suna zuwa EFCC bayan barin mulki, mu ne mutanen da muke tilasta musu tsintar kansu cikin hakan."
"Ni kuma ba zan bari a tilasta min ba. Zan yi abin da dokar ƙasa ta yarda da shi, abin da ba ta yarda da shi ba, zan kauce masa. To yanzu, wane asusu ko kasafin kuɗi nake da shi da zan cire kuɗi na bayar ga ƙungiyoyi?"

Kara karanta wannan
Gwamna Radda ya yi karatun ta natsu, ya fadi abin da zai hana magance 'yan bindiga
- Fasto Umo Eno
Gwamna Eno ya magantu kan shirin barin PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya nuna alamun cewa zai tattara ƴan komatsansa daga jam'iyyar PDP.
Gwamna Umo ya nuna alamun cewa zai bar jam'iyyarsa ta PDP na ba da jimawa zuwa wata jam'iyya da bai bayyana ba.
Umo Eno ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai fice daga jam'iyyar PDP duk da irin ƙaunar da yake yi mata a zuciya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng