'Akwai Babbar Barazana ga APC,' Babban Lauya Ya Fadi Abin da zai Kifar da Tinubu
- Babban lauya a kasar nan, Mike Ozekhome ya ce wahalar rayuwa da fushin jama'a na iya kifar da Tinubu a 2027, idan adawa ta hada kai sosai
- Ozekhome ya shawarci jam’iyyun adawa su yi abin da ya dace, domin zai ba su damar tabbatar zama babban kalubale ga gwamnatin APC
- Ya kara da cewa jama'a sun gaji da halin da gwamnati ta jefa su, wanda zai saukakawa hadakar adawa hambarar da gwamnati
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fitaccen lauya kuma masani a harkokin kundin tsarin mulki, Mike Ozekhome (SAN), ya bayyana cewa jam'iyyar APC za ta iya rasa kujerar shugaban kasa a 2027.
Hauhawar farashin rayuwa da rashin jin daɗin al’umma a mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya zama tushen kafa ƙawancen adawa da zai iya kifar da shi a zaben 2027.

Source: Facebook
The Punch ta wallafa cewa, idan aka yi haɗin kai da tsari mai kyau, to ragowar jam’iyyun adawa da ke da rauni a yanzu na iya samun nasarar doke jam’iyyar APC da Shugaba Tinubu a zaben gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Za a iya kifar da APC,’ Ozekhome
A jawabinsa, babban lauyan ya bayyana cewa jama'a sun gaji da yadda gwamnatin Bola Tinubu ta zuba ido ana cikin tsanani na rayuwa.
Ya ce wannan babban dalili ne da zai iya kawo cikas ga gwamnatin APC, musamman idan 'yan adawa suka hada kansu wuri guda.

Source: Facebook
Mike Ozekhome (SAN) ya ce:
“Tare da wahala da fushin jama’a da ke yaduwa a kasa, wata ƙwaƙwarar hadaka na iya kifar da shi (Tinubu) daga mulki."
Tinubu: Ozekhome ya shawarci jam’iyyun adawa
Ozekhome ya bukaci jam’iyyun adawa su hada kai, yana mai kwatanta tsarin siyasar Najeriya da na Amurka, inda jam’iyyun biyu ke musayar iko lokaci zuwa lokaci.
Ya ce:
“Ya kamata mu kafa irin wannan tsarin da ba zai bai wa kowace jam’iyya damar mamaye ƙasar gaba ɗaya ba.”
Haka ma wani lauya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Abdul Mahmud, ya goyi bayan ra’ayin Ozekhome, inda ya bayyana cewa manufofin tattalin arzikin Tinubu na jawo matsaloli.
Ya ce:
“’Yan Najeriya sun sha wahala a karkashin Tinubu kuma za su ci gaba da wahala idan ya ci gaba da bin wannan tsarin tattalin arziki irin na Turawan mulkin mallaka.”
Buba Galadima ya caccaki Tinubu
A wani labarin, mun wallafa cewa jigo a NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da al’amuran kasa.
Buba Galadima ya bayyana cewa ikirarin da Bola Tinubu ke yi na cewa ya samar da ci gaba a fannin tattalin arziki, tsaro da yaki da cin hanci ba su da tushe balle makama.
A jawabin da ya gabatar a ranar 29 ga watan Mayu, 2025, domin bikin cika shekaru biyu da hawa mulki, Tinubu ya ce gwamnatinsa na aiwatar da muhimman matakan samar da ci gaba.
Asali: Legit.ng

