'Cigaban Mai Haka Rijiya,' Buba Galadima Ya ce Babu Abin a Yaba a Shekaru 2 na Tinubu

'Cigaban Mai Haka Rijiya,' Buba Galadima Ya ce Babu Abin a Yaba a Shekaru 2 na Tinubu

  • Jigo a NNPP, Buba Galadima ya soki mulkin Bola Tinubu, yana cewa babu wani ci gaba da gwamnatin ta samar a cikin shekaru biyu
  • Wannan na zuwa a matsayin martani ga jawabin da shugaban kasar ya yi a lokacin da yake bayanan ayyukan gwamnatinsa bayan hawansa mulki
  • A martaninsa, Buba ya ce abubuwa da dama sun nuna gazawar gwamnatin Tinubu da suka hada da matsalar tsaro da durkushewar tattalin arziki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jigo a jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya bayyana rashin gamsuwarsa da mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana cewa yana da'awa da ikirarin da Shugaban Bola Tinubu na cewa gwamnatinsa ta yi abin arziki a cikin shekaru biyu da ya yi a kan mulki.

Kara karanta wannan

Shekara 2 a mulki: Fadar shugaban kasa ta kausasa harshe ga Atiku kan sukar Tinubu

Galadima
Buba Galadima ya bayyana cewa babu cigaba a gwamnatin Tinubu Hoto: Comr Ahmad/Bayo Onanuga
Source: Facebook

A martanin da Buba Galadima ya yi a hirarsa da BBC Hausa, ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a ikirarin da shugaban kasa ya yi na kawo ci gaban Najeriya.

Jawabin Bola Tinubu kan gwamnatinsa

Channels TV ta ruwaito cewa a ranar 29 ga watan Mayu, 2025, Shugaba Tinubu ya gabatar da jawabi na cika shekaru biyu da kama mulki.

Shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu gagarumin ci gaba musamman a fannin tattalin arziki, tsaro, yaki da cin hanci, da kuma rage yawan bashin da ake bin Najeriya.

Ya ce:

“Muna kafa tubalin ginin makoma mai ɗorewa a Najeriya, muna ƙirƙirar wani tsari da kowa zai amfana, ba tare da an bar kowa a baya ba."

'Ba mu ga komai ba,' Buba Galadima ga Tinubu

Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa darajar Naira a kasuwa ita ce mafi muni tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, inda ya ce a yanzu dala ɗaya na cin N1650.

Kara karanta wannan

Atiku ya tono manyan 'kurakuran' Tinubu a shekara 2, ya yi raddi mai zafi

Ya ce:

''Mu ba mu ga komai ba – mun ga cibaya domin abin da N10 za ta saya ma a da yau naira dubu ma ba za ta iya saya maka ba."

Dangane da ikirarin gwamnatin cewa farashin kayan abinci ya yi kasa, Buba Galadima ya nuna damuwa, yana cewa:

“Na yarda da maganar gwamnati cewa farashin abinci – shinkafa, alkama, masara ya yi kasa. Amma kai ka san abin da zai biyo baya?”
Tinubu
Buba ya ce an samu tabarbarewar tsaro a gwamnatin Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce yawan hare-haren 'yan bindiga da matsalolin tsaro sun hana manoma komawa gona, lamarin da ka iya jefa ƙasa cikin matsalar yunwa.

Amnesty Int'l ta soki gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Amnesty Int'l, ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gaza cika alkawarin kare rayukan jama'a.

Kungiyar ta ce a cikin shekaru biyu da suka gabata, fiye da mutane 10,217 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da kungiyoyin 'yan bindiga da masu tada kayar baya ke kai wa.

Rahoton ya ce jihar Binuwai ce ta fi fuskantar asarar rayuka, inda aka kashe mutane 6,896, yayin da jihar Filato ta zo na biyu da adadin mutane 2,630 da aka kashe a rikice-rikice da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng