Gwamnoni 36 Sun Nuna Damuwa bayan Ambaliya ta Ruguza Gidaje da Mutane a Neja

Gwamnoni 36 Sun Nuna Damuwa bayan Ambaliya ta Ruguza Gidaje da Mutane a Neja

  • Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana alhini kan ambaliyar da ta kashe mutane da dama a Mokwa, jihar Neja
  • Shugaban NGF, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce lamarin ya tayar da hankali, yana mai nuna goyon baya ga gwamnati da mutanen jihar
  • An yi asarar rayuka akalla 21 tare da barnar dukiyoyin miliyoyin Naira a ambaliyar da ta addabi garin Mokwa na jihar Neja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana alhininta da juyayi kan ambaliyar da ta faru a karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.

An ruwaito cewa mutane da dama ne suka rasa rayukansu tare da asarar dukiya mai yawa yayin da har yanzu ba a ga wasu ba.

Mokwa
Gwamnoni sun yi jimamin ambaliyar ruwa a Mokwa. Hoto: True Crime Daniel
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya fitar da wata sanarwa a madadin sauran gwamnoni.

Kara karanta wannan

2027: Wasu 'yan majalisa sun yi watsi da hadaka, sun goyi bayan tazarcen Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa sun shiga damuwa matuƙa lura da irin girman ibtila’in da ya faru.

Kungiyar ta ce tana tare da gwamna Umaru Bago da al’ummar jihar Neja a wannan lokaci mai cike da kunci da baƙin ciki.

Ambaliya ta kashe mutane 21 a Neja

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane fiye da 21 ne suka rasa rayukansu a ambaliyar da ta auku a garin Mokwa, inda ruwa mai ƙarfi ya yi barna ga gidaje da kadarori masu tarin yawa.

Kungiyar NGF ta bayyana cewa wannan bala’i ya zama ruwan dare da ya sauka a kan al’umma, yana mai tayar da hankali da kuma bayyana bukatar gaggauta daukar matakan kariya.

Gwamnoni sun yaba wa gwamnan Neja

Sanarwar NGF ta yabawa matakin da gwamnatin jihar Neja ta ɗauka cikin gaggawa, da haɗin gwiwar hukumomin agaji da ceto wajen taimakawa waɗanda abin ya shafa.

Gwamnonin sun ce wannan ambaliya ta sake jaddada buƙatar da ke akwai na haɗin kai da cibiyoyin gwamnatin tarayya kamar NEMA da ONSA don tunkarar sauyin yanayi da tasirinsa.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Mutum 12 daga gida daya sun rasu, ana zargin almajirai 50 sun nutse a Neja

Gwamna Bago
Gwamnoni yaba da matakin da Bago ya dauka bayan ambaliya a Neja. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

NGF ta nemi hadin kan jama’a da addu’o’i

Shugaban kungiyar ya nemi jama’a da su goyi bayan matakan da gwamnati ke ɗauka don rage illar sauyin yanayi da kuma taimakawa waɗanda ambaliyar ta shafa.

Ya kuma roƙi Allah Ya jikan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da bai wa danginsu da sauran al’umma hakuri.

AbdulRahman AbdulRazaq ya yi kira da a ci gaba da addu’a da haɗin kai don neman kariya daga irin wannan ibtila’in a gaba.

Daily Trust ta wallafa cewa an rasa mutane 12 a gida daya yayin da ake nemi almajirai sama da 50 aka rasa a sanadiyyar ambaliyar.

Ambaliya ta kashe malamin coci a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa ambaliyar ruwa ta jawo mutuwar wani limamin coci a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiyan Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne sakamakon ruwa mai karfi da aka yi a karamar hukumar Lapai ta jihar.

Legit ta rahoto cewa rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin tare da yin karin haske kan halin da aka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng