Babbar Sallah: Za a Raba Dubban Shanun Layya Kyauta ga Musulmi a Kano, Abuja da Jihohi 11
- Wata gidauniyar Turkiyya (TDV) za ta yi layyar shanu 6,000 domin rabawa musulmi nama kyauta a jihohi 11 da birnin tarayya Abuja
- Gidauniyar dai ta tsara rabawa talakawa, mabukata da masu ƙaramin karfi naman shanu 6,000 a lokacin shagalin babbar sallah
- Wannan na zuwa ne bayan fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta sanar da ganin jinjirin watan babbar Sallah a daren ranar Talata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Yayin da musulmi ke ci gaba da shirye-shiryen babbar sallah a makon gobe, wata gidauniya daga ƙasar Turkiyya za ta raba sadaƙar nama.
Gidauniyar mai suna, Turkiye Diyanet Foundation (TDV) ta kammala shirin layya da shanu 6,000 a jihohi 11 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Source: Getty Images
Jaridar The Nation ta tattaro cewa za a rabawa Musulmai marasa ƙarfi da masu buƙata naman waɗannan shanu 6,000 a lokacin bikin Sallar Layya (Eid al-Adha).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Musulmi ya sanar da ganin wata
Wannan dai na zuwa ne bayan mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III ya tabbatar da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah ranar Talata.
A sanarwar da fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato ta fitar a daren Talata, Sultan ya ayyana ranar Laraba, 28 ga watan Mayu a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah, 1446H.
Hakan dai na nufin al'ummar musulmin Najeriya za su yi sallar idin layya ranar Juma'a, 10 ga watan Dhul Hijjah, 1446H wanda zai yi daidai da 6 ga watan Yuni, 2025.
Gidauniya za ta raba shanu a Abuja, jihohi 11
Bayan haka ne gidauniyar Turkiyya ta bayyana shirinta na yanka shanu 6,000 domin raba sadaƙar nama ga talakawa da mabukata a jihohi 11 da Abuja.
An ruwaito cewa za a raba naman shanun ne a cikin jihohin Bauchi, Oyo, Sokoto, Gombe, Kano, Nasarawa, Filato, Kaduna, Kogi, Niger, Jigawa da kuma FCT Abuja.
Wannan aikin layya yana daga cikin manya-manyan ayyukan jin ƙai da gidauniyar TDV ke yi da nufin rage yunwa da tallafa wa al’ummomin Musulmai.

Source: Getty Images
Taimakon da TDV take yi wa musulmai
Sauran ayyukan da gidauniyar ke gudanarwa sun haɗa da, gina masallatai, ciyar da masu azumi lokacin buɗa baki a watan Ramadan, d samar da ruwa mai tsafta ta hanyar haƙa rijiyoyi.
Sauran ayyaukan taimakon al'umma da gidauniyar ke yi sune, ba da tallafin karatu ga ɗalibai da kuma aikin tiyata kyauta ga marasa ƙarfi.
Wannan ya nuna cewa gidauniyar TDV na ci gaba da tallafawa al’ummar Musulmai a Najeriya, musamman a lokacin bukukuwa na ibada.
Talakawa sun sayawa gwamna ragon layya
A wani labarin, kun ji cewa mazauna unguwar Nayinawa a Gombe sun yi karo-karo, sun saya wa Gwamna Inuwa Yahaya ragon da zai yi layya da sallah.
Mutanen unguwar sun yi haka ne domin nuna godiya ga mai girma gwamnan bisa aikin cike wani kwari da ke hana shiga yankin, wanda aka kammala kwanan nan.
Kwarin da ke cikin unguwar Nayinawa ya kasance babban kalubale ga mazauna yankin, inda yake hana su zirga-zirga lokacin damina.
Asali: Legit.ng

